Mayakan Jibhatun Nusra Sun Kai Hare-Hare Kan Yankunan Tudun Tsira A Kasar Siriya.
Majiyoyin gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’adda na Jibhatun Nusra sun kai hare-hare a yankunan tudun tsira na arewacin kasar Siriya a daren jumma’an da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Jibhatun Nusra sun keta hurumin yarjiniyar da aka cimma da ita tare da taimakon gwamnatin kasar Turkiya a daren jiya jumma’a, inda suka kai hare-hare kan wasu yankuna a lardun Halab, Idlib da kuma Lazukiyya.
Labarin ya kara da cewa lardunan Halab, Hamah da Lazikiyya suna daga cikin yankunan tudun tsira a kasar ta Siriya, kuma a cimma yarjeniya da wadannan ‘yan ta’adda wadanda suka yi ta shan kaye a hannun sojojin siriya da kuma mayakan mukawama kan cewa su tudun tsira ne.
READ MORE : Gwamnatin Buhari Ta Bada Kontiragin Kula Da Tsaron Layin Dogo Da Tashoshinsa.
Lardin Idlib na kasar Siriya ne kawai lardin da har yanzun yake karkashin ikon ‘yan ta’adda na Jabhatun Nusra da kuma Jaish Tahriru sham a kasar Siriya. Kuma ba wannan ne karon farko wanda suke keta hurumin yarjeniyar ba.
READ MORE : NNPC; Najeriya Za Ta Daina Shigo Da Tataccen Man Fetur Daga Waje A 2022.