Mayakan Boko Haram sun kai farmaki sansanin sojojin Kamaru a ranar Asabar inda suka kashe mutum bakwai tare da raunata da dama.
Sun kai harin a sansanin soji da ke Sagme a yammacin ranar Asabar kamar yadda sojoji suka sanar.
Mayakan , dauke da muggan makamai sun yi shigar burtu da kakin soja a ababen hawa shida.
Bayan share awanni ana artabu da su, mayakan sun kashe kwamandan sojojin tare da dakarunsa shida.
“Sojojin sun yi namijin kokari wajen daukar lokaci suna artabu da ’yan ta’addan.
“Dole a jinjina musu kan yadda suka yi kokarin dakile harin tare da ceto rayukan wasu da dama,” a cewar wani da ya bukaci a sakaya sunansa.
Rundunar sojin ta ce ta jikkata da dama daga cikin mayakan amma ba ta bayyana adadinsu ba.
Harin na ranar Asabar na daga cikin mafiya muni da aka kai wa rundunar sojin Kamaru cikin wata 10 da suka wuce, a cewar rahoton rundunar sojin kasar.
Tun a shekarar 2014 Boko Haram take kai hari a Arewacin kasar Kamaru, inda ta kashe akalla mutum 2,000, a cewar rahoton rundunar.
A wani labarin na daban Gwamnatin Tarayya a ranar Asabar ta damka wa kananan manoman rani a Karamar Hukumar Auyo ta Jihar Jigawa wasu ayyuka da darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 10.
Shirin, wanda ya kunshi kadada 2,000 na gonaki wanda yake samun tallafin Bankin Duniya an bullo da shi ne da nufin taimaka wa manoman yankunan karkara su ci gaba da noma tsawon shekara ba kakkautawa.
’Yan bindiga sun yi awon gaba da takardun jarabawar NECO a Kaduna
Buhari zai gina gidajen yari a Kano da wasu jihohi
Hukumar Bunkasa Kogunan Hadeja da Jama’are (HJRBDA) ce dai take kula da shirin.
Da yake mika aikin ga Gwamna Badaru Abubakar na Jihar a kauyen Yamdi, Ministan Ruwa, Injiniya Sulaiman Adamu ya bayyana kammala aikin a matsayin cika alkawarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauka yayin wata ziyara a 2018.
A cewar Ministan, akalla kananan manoma 200 ne ake sa ran za su amfana da shirin.Ya ce a tashin farko, aikin ya lashe Naira biliyan 9.3 ne, sai daga bisani aka kara Naira biliyan 1.48.
Minista Sulaiman ya ce ya zuwa yanzu aikin ya kai matsayin kaso 74 cikin 100 na kammalawa, inda ake sa ran nan da watan Yunin badi za a kammala shi baki daya.