Hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya, ta yi gargadin cewa matsalar gurbacewar muhalli da canjin yanayi, na tasiri wajen kara rura wutar tashe-tashen hankula a fadin duniya, matsalar da ta ce nan kusa za ta zama kalubale mafi girma ga kare hakkin dan adam.
A cewar Bachelete halin da ake ciki ya zama abin tsoro ne, ganin yadda akasarin kasashe ba sa daukar matakan da suka dace wajen kawo karshen matsalar.
Bachelete ta kara da cewar tuni matsalolin na gurbatar muhalli da canjin yanayi suka fara dakile jerin hakkokin dan adam da suka hada da samun isasshen abinci, ruwa, ilimi, gidaje, lafiya, ci gaba, har ma da rayuwar kanta.
Zalika gurbacewar muhallin galibi yafi cutar da al’umomin kasashe matalauta sakamakon rashin karfinsu na daukar matakan ware-ware matsalolin.