Matsalar Abinci; EU Na Shirin Janye Wasu Takunkumai A Kan Bankunan Rasha.
Kungiyar Tarayyar Turai na shirin dage wasu daga cikin takunkuman da ta kakaba wa bankunan kasar Rasha domin ba da damar cinikin abinci.
Kamfanin dillancin labaran “Reuters” ya bayar da rahoton cewa, Tarayyar Turai tana da shirin fitar da wasu bankunan Rasha daga cikin bankunan da ta kakaba wa takunmi ne, saboda suna da alaka kai tsaye da harkokin cinikin abinci, daga cikinsu akwai bankin (VTB), Sovcom bank, Novicombank, Otkrytie, (FEB) VEB, Promsvyaz, Russia Bank.
Sannan Tarayyar Turai za ta saka wani sabon takunkumi a kan kadarorin Sberbank, babban bankin Rasha, in ban da bankunan da suka dace da cinikin abinci, wanda a yau ne Laraba 20 ga watan Yuli matakin zai fara aiki.
Kamar yadda daftarin ya nuna, kasashen turai za su iya cire kudi a wadannan bankuna, bayan tabbatar da cewa abubuwan da ake bukata wajibi ne a shigo da su, ko kuma yin jigilar kayan amfanin gona da abinci, gami da alkama da takin zamani daga kasar ta Rasha.
Kuma wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen Afirka ke sukar lamirin takunkumin da aka kakabawa kasar Rasha kan harkokin kasuwancin duniya, wanda zai iya haifar da karuwar matsanancin karancin abinci a duniya.
Yanzu haka dai kasashen turai da dama sun shiga cikin matsaloli sakamakon takunkuman da suka dora wa Rasha, musamman kasashen da Rasha ta dakatar da sayar musu da makamashi, daga ciki har da kasashen Jamus da Burtaniya, wanda hakan yasa yanzu haka wasu kamfanonin wadannan kasashe sun daina aiki baki daya.