A karon farko cikin shekaru biyu, mata a Iran za su halarci filin wasan kwallon kafa da ke birnin Tehran domin nuna goyon bayansu ga tawagar kasar wadda za ta kara da Koriya ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Raban da matan Iran su halarci filin wasan tun cikin watan Oktoban 2019, lokacin da Iran din ta lallasa Cambodia da kwallaye 14-0.
Kafin wannan lokaci, hukumomin Iran sun haramta wa mata shiga filin wasan a shekara ta 1979 domin kare mutuncinsu da kuma hana su cakuduwa da maza.
Amma Hukumar Kwallon Kafa ta Duniuya ta yi wa Iran matsin lamba don ganin ta janye dokar hana su shiga filin wasa, sai dai hukumomi a Iran din sun nuna tirjiya a kokarin su na tabbatar da mutuncin mata a kasar gami da tabbatar da cewa matan sun sami cikakkiyar kulawa gami da kare mutuncin su.
Cakuduwar maza da mata na cikin abubuwan da kan zubar da mutuncin matan a idanun maza kuma hakan kan haifar da matsalli da suka hada da cin zarafin matan kamar yadda yake yawan faruwa a kasashen yammacin turai.
A kokarin su na tabbatar da walwala cikin ‘yanci gami da kare mutuncin mata hukumomi a Iran kanyi duk mai yiwuwa domin tabbatar da hakan ko da hakan ya sabawa muradan hukumomin duniya.
Bincike ya tabbatar da cewa babu wata kasa da mata ke samun cikakkiyar kulawa gami da walwala da ‘yancin gudanar da lamurra ba tare da tsangwama irin Iran.
Mata kanyi ayyukan jarida koyarwa, likitanci da dai sauran su kuma suna da dama daya a banagren samun guraben karatu a jami’a, abu mafi muhimmanci kuma basu da tsoro ko firgici dangane da kiyaye mutuncin su, sabanin kasashen yammacin turai da mata ke cikin fargaba da tsoron keta musu mutunci a kowanne lokaci.