Kungiyar masu rajin kare auren jinsi a Faransa na shirin maka dan takarar shugabancin kasar mai tsattsauran ra’ayi Eric Zemmour kotu, saboda zargin sa da karyata cewa an yiwa masu auren jinsi kawanya lokacin da dakarun Nazi suka mamaye Faransa a yayin yakin duniya na biyu.
A cikin wani tsokaci na Zemmour da aka wallafa, wanda cikin sa ne ya yi wadannan kalamai, dan takaran ya kuma amince da wani dan siyasa da ya bayyana ikirarin cewa a ci zarafin masu auren jinsi a matsayin al’amara.
Kungiyoyin masu kare jinsin na faransa sun kuma dage kan cewa Zemmour ya bijiro da wadannan kalamai ne don kawai ya sake jaddada tsattsauran ra’ayin da yake da shi.
Sai dai kuma tuni Lauyansa Olivier Pardo ya ce bai ma sami takaradar koken a hukumance ba, yana mai cewa wadannan kalamai, ba wai kai tsaye sun fito daga bakin wanda ya ke karewar ba, sai dai kawai ya amince ne da su, kuma yana da damar yin hakan.
A wani labarin na daban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki manyan kasashen duniya, inda ya ce sun aikata babban laifi saboda yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu. Kalamansa na zuwa ne bayan fitar da wani sabon rahoto kan illolin sauyin yanayi, inda ya zargi manyan kasashen da ta’azzara matsalar.
Rahoton ya kuma bukaci tuhumar wadannan manyan kasashe na duniya saboda yadda suka gaza wajen daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar.
Mista Guterres ya bayyana cewa, kusan rabin al’ummar duniya na rayuwa cikin gagarumar barazana a yanzu, yayin da sukurkucewar alaka tsakanin halittu da muhalli ta kai matakin kololuwa a cewarsa.
Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, babu yadda za a karyata batun cewa, lallai hayaki mai gurbata muhalli shi ne ummul-haba-i-sin sauyin yanayin.
Sannan ya ce, watsi da nauyin da ya rataya akan shugabannni na matsayin babban laifi, kuma manyan kasashen duniyar da suka fi gurbata muhalliu, su ne da laifin cin amanar doran duniyar da muke rayuwa a ciki a cewarsa.
An dai fitar da rahoton kwararrun ne na Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da rikcin Rasha da Ukraine ke daukar hanklulan kasashen duniya.