Masar Zata Sayarwa Kasar Poland Da Wasu Kasashen Turai Iskar Gas.
Shugaban kasar Poland Andrezej Duba ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta cimma yarjejeniya da kasar Masar don sayan iskar gasa daga kasar.
Jaridar Egypt today ta nakalto shugaban yana fadar haka a a jiya litinin a lokacinda yake jawabin hadin giwa da shugaban kasar Masar Abdulfattah Assi a birnin Alkahiri.
Labarin ya kara da cewa shuwagabannin biyu sun tattauna batutuwan da zasu karfafa dangantakar kasashen biyu a ko wani fanni.
Yakin da ake a Ukraine, ya tilastawa kasashen Turai haramtawa kansu amfani da iskar gas na kasar Rasha, don haka ko wanne daga cikinsu na neman inda zata sayi iskar gas don tabbatar da takunkuman tattalin arzikin da suka dorawa kasar Rasha suna aiki.
READ MORE : Sudan; An Saki Wasu ‘Yan Zanga-Zangar Da Aka Kama A Kasar Sudan A Jiya Litinin.
A cikin watan fabarairun da ya gabata ne kasar Rasha ta farma Ukrain da yaki don tabbatar da ‘yencin yankin Dombas na kasar Ukrain da kuma tabbatar da cewa Ukrain bata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba.
READ MORE : Majalisar Dokokin Yemen Ta gabatar Bukatar Kafa Doka Ta Haramta Hulda Da Isra’ila.