Hukumar kwallon kafa ta Masar ta shigar da kara a hukumance kan Senegal inda ta ce jami’ai da ‘yan wasanta sun fuskanci cin zarafin wariyar launin fata da kuma firgitarwa a lokacin da suke shirin buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a ranar lahadi.
Zalika an rika jifan ‘yan wasan na Masar da kwalabe da duwatsu a lokacin da suke gudanar atasaye gabanin fara fafatawar da suka yi da takwarorinsu na Senegal.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, “An kai wa motocin bas din tawagar Masar hari, wanda ya yi sanadin farfasa tagogin su tare da jikkata wasu mutane, abinda ya sanya su shigar da kara gaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
A zagayen farko na karawar da suka yi an tashi babu ci 0-0 a Ghana, yayin da kuma a Najeriya aka tashi 1-1, abinda ya baiwa ‘yan wasan na Black Stars damar zuwa gasar cin kofin duniya ta bana.
Gabanin fara gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afirka ne dai hukumar kwallon Najeriya ta sanar da korar tsohon kocin Super Eagles Gernot Rohr, inda ta nada Austine Eguaveon a matsayin kocin rikon kwarya, inda kuma aka sa ran bayan kammala gasar ta AFCON mai yiwuwa a sanar da Jose Pasiero tsohon kocin kungiyar FC Porto da ke kasar Portugal a matsayin kocin dindindin na kwallon Najeriya.
Sai dai kash, al’amura basu tafi kamar yadda aka tsara ba, kasancewar Najeriya. ta fice daga gasar cin kofin ta Afirka tun a zagaye na biyu, bayan rashin nasara a hannun Tunisia da 1-0.
Shi kuwa Pasiero da akai ta sa ran shi ne zai zama kocin dindindin, daga bisani hukumar NFF ta bayyana cewar babu wata yarjejeniya da aka cimma tsakaninsu da jami’in, wanda ya gaza bayyana a Kamaru domin sa idanu kan yadda wasannin Najeriya za su kaya a matsayin dan kallo, kafin ya soma jagorantarsu.