Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar Masar sun sanar da cewa, rufe wannan mashigar yana da alaka ne da shiga tsakanin da Kasar Masar take yi tsakanin Isra’ila da kuma kungiyar Hamas.
Haka nan kuma wani daga cikin jami’an gwamnatin kasar ta Masar ya ce, an dauki wannan matakin ne da nufin yin matsin lamba a kan kungiyar Hamas dangane da batun dakatar da bude wuta tsakaninta da Isra’ila, kamar yadda kuma ya bayyana cewa ba a san har zuwa wane lokaci ne mashigar ta Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe ba.
Mashigar Rafah dai ita ce babbar mashigar da ake shigar da kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin Zirin Gaza, wanda Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza suke yin amfani da ita domin ci gaba da rayuwa.
Gwamnatin kasar Masar tana yin amfani da mashigar Rafah domin yin matsin lamba akan Falastinawa musamman ma kungiyoyin gwagwarmaya na yankin zirin Gaza, inda ta kan rufe wannan mashiga a duk lokacin da ta ga dama, domin yin matsin lamba a kansu domin su amince da wasu bukatu na Isra’ila ko kuma wasu kasashen na daban.
A wani labarin na daban hafin yada labarai na Albayan ya bayar da rahoton cewa, Ibrahim Muhammad Bumalha babban mai bayar da shawara ga sarkin Dubai kan harkokin addini ya sanar da cewa an fara rijistar sunayen mata masu shawar shiga gasar kur’ani ta duniya ta mata a kasar Hadaddiyar daular Larabawa, wadda ake yi wa taken gasar kur’ani ta Shaikha Fatima Bint Mubarak.
Ya ce sakamakon matsaloli na kiwon lafiya musamman cutar corona da ta addabi duniya, wannan ne yasa aka aka jinkirta gudanar da gasar.
Dangane da gasar a bangaren maza ya ce an samu damar gudanar da ita a cikin watan ramadan da ya gaba cikin nasara.
Za a kammala rijistar sunayen wadanda suke son shiga gasar daga nan zuwa 15 ga watan Satumba mai kamawa, sannan za su iya ziyartar shafin yanar gizo na: [email protected] یا [email protected]
Sannan kuma ya bayyana sharudda na gudanar da gasar a bangaren mata wadda za a gudanar a nan gaba, inda ya ce mata da suke bukatar shiga gasar dole ne su kasance mahardata kur’ani da kuma sanain hukunce-hukunce na karatun kur’ani wato tajwidi, sannan shekarunsa kada su wuce 25 da haihuwa.