Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa, tun kafin wannan lokacin an bayar da sanarwa ga masu kula da wannan masallaci kan daukar matakan kiwon lafiya, amma ba su kula ba, saboda haka daga karshe dai an rufe masallacin sai abin da hali ya yi.
Tun bayan bullar cutar corona wannan masallaci yana daga cikin masallatai na farko da aka fara rufewa, kafin daga baya aka bude shi.
Ana danganta wannan wuri ne dai Sayyid Zainab amincin Allah ya tabbata a gareta diyar Fatima Zahra (AS) diyar manzon Allah (SAW) inda wasu ke cewa a tarihi bayan kisan Imam Husssain (AS) da zuriyar manzon Allah (SAW) da sojojin Yazid dan Mu’awiya suka yi a Iraki, a lokacin da za a kai su Zainab zuwa fadar Yazid a Sham, sun yada zango a Masar, yayin da wasu ke cewa ta rasu a Masar, amma dai ingantattun ruwayoyi sun tabbatar da cewa ta rasu ne a Damascus.
A wani labarin na daban kafofin yada labaran Falastinu sun sanar da cewa, mai magana da ywun ofishin shugaban kasar Masar Bassam Radhi ya sanar da cewa, ana shirin fara aikin gina yankin zirin Gaza nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ya ce wannan yana daga cikin ajandar taron da aka gudanar a cikin wannan mako, wanda ya hada shugaban kasar Masar Abdulfattah Al sisi da kuma shugaban Falastinawa Mahmud Abbas, da kuma sarkin Jordan Abdullahi na biyu a yankin Sharm Al Sheikh na kasar Masar.
Bassam ya ce, a yayin zaman, dukkanin shugabannin uku sun jadda matsayarsu taki amincewa da mamayar da Isra’ila take yi wa birnin Quds, tare da jaddada cewa wajibi ne a warware matsalar mamayar Falastinu da Isra’ila take, domin kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta, da babban birninta na Quds.
Sannan kuma kakakin fadar shugaban kasar ta Masar ya kara da cewa, nauyi ne day a rata a kan dukkanin kasashen duniya da su matsa lamba kan Isra’ila domin ta amince a kawo karshen wannan matsala.
A kan haka ne ma ya cea zaman shugabannin kasashen uku, an tattauna yadda za a koma tattaunawa tsakanin Falastinawa da Isra’ila, ta yadda hakan zai share hanyar komawa zuwa ga tattauna batun kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta.
Wasu rahotanni da kafofin yada labaran Isra’ila suka bayar sun ce, Masar da Qatar suna matsa lamba kan Hamas, kan ta dakatar da ayyukan da k tayar da hankalin yahudawa a kan iyakokin Gaza da Isra’ila, idan ta yi a nata bangaren Isra’ila za ta bude iyakokin Gaza domin shigar da abinci da sauran kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin.
Sai a nata bangaren Hamas ta ce duk wani batyun tattaunawa da Isra’ila ko yin aiki da sharuddan da Isra’ila ta gindaya, hakan bai shafe ta ba kuma bai shafi al’ummar Gaza ba, idan Isra’ila ta yi wani shishigi kan yankin zirin Gaza, to za ta fuskanci martani.