Masar Ta Karyata Batun Cewa; Tana Hana ‘Yan Sudan Shiga Kasarta.
Gwamnatin Masar ta kore batun da ake yadawa cewa: Tana hana wasu ‘yan Sudan shiga cikin kasarta.
A bayanin da babban jami’i a karamin ofishin jakadancin Masar da ke Sudan Ahmad Adli ya fitar ya bayyana cewa: Ofishin jakadanci Masar da ke kasar Sudan bai fitar da wata sanarwa kan hana ‘yan Sudan shiga cikin kasar Masar ba, iyaka dai wasu bangarori ne da ba a san ko su wane ne ba da suke son bata alakar da ke tsakanin kasashen biyu suke yada irin wannan jita-jita maras tushe.
READ MORE : Kasar Iran Ce Kan Gaba A Fagen Yaki Da Muggan Kwayoyi A Duniya.
Jami’in ofishin jakadanci na Masar ya kara da cewa: Tabbas babu wani batun neman hana ‘yan Sudan da suke ‘yan uwan juna ne ga Misrawa shiga kasar Masar, yana mai jaddada kyakkyawar alaka da soyayya da suke tsakanin al’ummun biyu wacce Masar gida ce ga ‘yan Sudan.
READ MORE : Sojojin Amurka da na Birtaniya sun shiga tashar ruwan Nastoun na kasar Yamen.
READ MORE : Dole Burtaniya Ta Shirya Yaki Da Rasha – Sojin Burtaniya.
READ MORE : Rivers : Kotu ta ba da Belin Ɗan Majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare.