Wani mai nazari ya ce soki burutsu da karin gishiri a miya ne kawai ake yi game da cewar wai Masar na shirin kafa wani yankin mafaka a Falasdinawan da suka gudu daga Rafah.
Akwai katanga tsakanin Rafah da Masar, a yayin da ake fargabar kwararar Falasdinawa zuwa Masar. A Rafah, Kudancin Gaza, 16 ga Fabrairu, 2024.
A yayin da Isra’ila ke ci gaba da yin barazanar kai hare-hare a Rafah, Masar kuma na fuskantar suka kan rahotannin da kafafen watsa labarai suka fitar na cewa tana shirin gina katanga akan iyakarta da manufar katange Falasdinawan da hare-haren soji suka raba da matsugunansu.
An dinga yawan azarbabi game da sukar da ake ma Masar, a yayin da kasar ke ci gaba da nuna adawa da tirsasawa Falasdinawa su bar matsugunansu, kuma ta ke kokarin ganin Isra’ila ta dakatar da mamaya.
Kasar na kuma shirin tunkarar kusantar iyakarta, tane aikin taimaka wa Falasdinawa mabuƙata.
Da yake mayar da martani kan shirin kan iyakar a makon da ya gabata, Diaa Rashwan, shugaban Hukumar Sadarwa ta Masar (SIS) ya ce, raba Falasdinawa da matsugunansu “na nufin hana tabbatar da burinsu, kuma barazana ce kai tsaye ga ƙarfin iko da tsaron kasar Masar.”
Wasu hotuna da bidiyo da kungiyoyin sanya idanu da mafufuta suka fitar sun nuna ana gudanar da manyan ayyukan gini a bangaren Masar na kan iyakar Rafah, ciki har da katangun kankare da kuma baje kasa. Amma babban jami’in diplomasiyyar Masar ya yi watsi da zargin, yana mai cewa ‘Masar na gina wani waje ne kawai na karbar Falasdinawan da aka raba da matsugunansu”.
DUBA NAN: Sudan Kasa Mafi Yunwa A Afirka
“Ba za mu kalli wannan shaci fadi ba. Kuma za mu ci gaba da yin kira ga dukkan kawayenmu, dukkan wadanda suka fahimci rikita-rikita da hatsarin da ke tattare da wannan batu, sannan muna bayyana cewa dole za a samu sakamako mara daɗi idan aka raba mutane da matsugunansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry.