Kasar Masar na karbar bakoncin ganawar shugabannin Isra’ila da na Hadaddiyar Daular Larabawa don yin wasu shawarwarin da ba a taba gani ba, daidai lokacin da yakin Ukraine ke ruguza kasuwannin makamashi da abinci da kuma manyan kasashen duniya wajen cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Masar, Haramtacciyar kasar Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa kawayen Amurka ne amma kawo yanzu sun kaucewa daukar matsaya kan Rasha game da yakin da ta ke yi da Ukraine.
Sanarwar da ofishin firaministan Isra’ila Naftali Bennett ta fitar ta ce, sakamakon abubuwan da suka faru a duniya, shugabannin sun tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen uku da kuma hanyoyin karfafa su a dukkan matakai.
A ganawar da suka yi, shugabannin uku sun tattauna kan batun makamashi, harkokin kasuwanci da kuma yadda za a inganta hanyoyin samar da abinci da kuma yadda za’a fuskanci barazanar raunanan falasdinawa.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce shugabannin za su kuma tattauna kan rahotannin da ke cewa Iran da manyan kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka na daf da farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015.
Isra’ila dai na adawa da yarjejeniyar da aka kulla domin hana babbar makiyiyarta wato Iran mallakar makamin nukiliya, burin da kasar ta ke musantawa a ko da yaushe.
A wani labarin na daban Amurka ta sanya takunkumai a kan shugabannin wasu kungiyoyin ‘yan daba guda biyu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakamakon rawar da suke takawa wajen tunzura jama’a da rikicin kasar mai nasaba da kabilanci da addini.
Sannan takunkumin ya haramtawa Amurkawa da kamfanonin kasar yin hulda da mutanen inda aka kuma rufe asusun ajiyarsu a Amurka.
Rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ya kashe daruruwan mutane tare da raba dubbai da gidajensu.
An zargi mutanen ne da kokarin yamutsa kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulki da gudanar a 2015 tare da yin zagon kasa ga jagorancin shugaba Faustin-Archange.