Masar ta fito fili ta hada kanta da Somaliya sannan kuma a boye da Eritriya tana adawa da Habasha. GERD yana da mahimmanci ga Habasha, wanda ke ba da gudummawar akalla kashi 85 na ruwan kogin Nilu. Wannan ya sanya madatsar ruwa ta zama mai muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikinta.
Dogaro da Masar ga yerjejeniyar da ba ta daɗe ba—yarjejeniya ta 1929 da yarjejeniyar 1959—ba ta nuna ainihin yanayin siyasa na yanzu ko kuma buƙatun ƙasashe masu tasowa kamar Habasha. Tsofaffin yarjejeniyoyin, hade da sauye-sauyen baya-bayan nan na kawancen kasashen yankin da tashin hankali, sun haifar da yanayi da ka iya haifar da rashin kwanciyar hankali a kan ruwan Nilu.
Daga Yuli 2014 zuwa Agusta 2022, Sudan ta Kudu da Uganda sun kasance kawayen yankin Masar, suna goyon bayan dabarun Alkahira. Sai dai Masar ta fuskanci kalubale wajen aiwatar da dabarunta na yaki da Habasha a Sudan ta Kudu saboda gagarumin adawar da take yi na cikin gida, musamman daga al’ummar Nuer da ke da alaka ta tarihi da Habasha.
Duba nan:
- Volkswagen Polo yanzu ya fito daga Afirka ta Kudu
- Egypt could spark regional conflict over Ethiopia’s dam
A baya-bayan nan, Somaliya da Eritriya, wadanda a da ba su da alaka da juna, sun sauya matsayinsu saboda sauyin yanayin siyasa. Mahimman abubuwa guda biyu ne ke tafiyar da daidaitarsu da Masar. Da farko, Somaliland – yanki mai cin gashin kansa a cikin Somaliya wanda ba shi da amincewar kasashen duniya – ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Habasha a bana.
Wannan yarjejeniya dai ta baiwa Habasha damar shiga tashoshin jiragen ruwa a Tekun Aden da kuma Tekun Bahar Maliya. Gwamnatin Somaliya, wacce ta dauki Somaliland a matsayin wani yanki na kasarta, tana kallon yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Somaliland da Habasha a matsayin barazana ga diyaucinta. Sakamakon haka, Somaliya ta yi barazanar yin amfani da dukkan matakan da ake da su, da suka hada da matakin soji, don hana Habasha amfani da wadannan manyan tashoshin jiragen ruwa ta Somaliland. Wannan sauyi ya yi tasiri sosai kan daidaitawar Somaliya da Masar, yayin da duka biyun ke neman tinkarar tasirin da Habasha ke da shi.
Na biyu, kungiyar fano, wata kungiyar kabilanci mai dauke da makamai daga yankin Amhara ta Habasha, ba ta gamsu da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Nuwamban 2022 tsakanin gwamnatin Habasha da kungiyar ‘yan tawayen Tigray People’s Liberation Front (TPLF).
Bayan yarjejeniyar zaman lafiya, mayakan Fano na ganin cewa firaministan Habasha Abiy Ahmed ya yi watsi da ajandar kawo sauyi kuma ya yi imanin cewa bai kamata a bar kungiyar ta TPLF ta kasance a matsayin kungiyar siyasa ba.
Sakamakon haka ne mayakan na Fano suka kafa babban sansaninsu a kasar Eritriya, inda suke samun horo da goyon bayan sojoji. Ita ma Eritrea, ba ta gamsu da shawarar Habasha na sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar TPLF ba.