Masanin kimiyya dan Pakistan wanda ya samar da makamin Nukiliya Abdul Qadeer Khan dake a matsayin gwarzo a kasar ya rasu ya na mai shekaru 85. Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar a yau lahadi,masanin ya share lokaci ya na jiya bayan kamuwa da cutar covid 19.
Shugaban kasar ta Pakistan Arif Alvi a wani sako ta kaffar twitter ya bayyana alhinin sa tareda isar da sakon ta’azziya zuwa iyalan mammacin da yan kasar ga baki daya.
A wani labarin na daban, Shugaban kasar China, Xi Jimping ya yi bikin tuni da zagayowar ranar juyin juya hali ,shekaru 110 da suka gabata ya dau daukar alkawalin sake hada tsibirin Taiwan da kasar ta China.
Taiwan dake da yawan al’uma da suka kai milyan 23 na rayuwa ne cikin barazanar China da kan iya mamaye ta a duk lokacin da ta ga dama.
Shugabar a karshe ta na mai cewa ,fatan kowace kasa shine na kasancewa cikin zaman lafiya da makwabta.