Masana harkar kwallon kafa a Turai na ci gaba da bayyana goyan bayan su na ganin ‘dan wasan gaba na Faransa dake yiwa kungiyar Real Madrid wasa Karim Benzema ya lashe kyautar Ballon D’Or ta bana da ake baiwa ‘dan wasan da yafi kowa fice kowacce shekara.
Arsene Wenger, tsohon manajan kungiyar Arsenal dake aiki da Hukumar FIFA yace a wannan shekarar babu ‘dan wasa guda da yafi Benzema fice, saboda haka ya dace a bashi lambar.
Zinadine Zidane, tsohon manajan kungiyar Real Madrid ya bayyana Benzema a matsayin wani taruraron da shi zai bashi wannan kyautar saboda ya dace a bashi.
Zidane ya bayyana tauraron Madrid a matsayin fitaccen’dan wasan da yayi nasarar horar da shi, kuma yanzu haka yake kan ganiyar sa.
Zidane ya bayyana fatar ganin masu zaben gwarzon shekarar sun zabi Benzema a wannan shekarar mai karewa.
Shi kuwa ’dan wasan gaba na kungiyar Manchester City Riyad Mahrez cewa yayi, babu wasu kalaman da za’a iya amfani da su wajen bayyana rawar da Benzema ke takawa kungiyar sa ta Real Madrid.
Mahrez yace kwashe shekaru 10 zuwa 11 da Benzema yayi yana sanye da riga mai lamba 9 a Real Madrid ta isa ta zama shaidar irin gudumawar da yake bayarwa wajen jefa kwallaye da kuma nasarorin da kungiyar ke samu, saboda haka ya dace a bashi kyautar bana.
Shi kuwa Roberto Carlos, tsohon ’dan wasan Brazil da kungiyar Real Madrid cewa yayi, koda a wata kungiya Benzema yake ba Madrid ba, zai zabi Benzema domin lashe kyautar a wannan shekarar.