Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta mayar da kakkusar martanin dangane da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa kan kasar Syria, da kuma yadda duniya ta yi gum da bakinta kan hakan.
Martanin na kungiyar Hizbullah ya ce, Isra’ila tana yin amfani da damar da ta samu wajen aikata abin da ta ga dama, ba tare da wani ko wata kasa ta isa ta ce uffan ba, saboda goyon bayan da take da shi daga gwamnatin Amurka, da hakan ya hada har da kai hare-hare a kan kasashen da ta ga dama.
Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyar kasar Lebanon wajen kai wa kasar Syria hari a jiya Alhamis, amma har yanzu babu wani martani daga bangarori na kasa da kasa kan hakan.
A jiya Alhamis ne dai Isra’ila ta kai hare-hare a yankin Qusair da ke cikin gundumar Homs a kasar Syria, inda ta harba makamai masu linzami a kan wasu wurare na sojin kasar, amma makaman kariya na rundunar sojin kasar Syria sun kakkabo dukkanin makaman da Isra’ila ta harba.
A wani labarin na daban shafin yada labarai na jaridar Alwafd ya bayar da rahoton cewa, Ibrahim najm mataimakin babban mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana cewa, an kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da taron fatawa ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.
ya ce a halin yanzu dai wakilan kasashe 85 ne za su halarci taron na kasa da kasa kan fatawa a kafofin sadarwa na zamani da zai gudana a ranakun 2 da kuma 3 ga watan Agusta mai kamawa.
Taron wanda na karawa juna sani ne, zai samu halartar masana daga wadannan kasashe, wadanda za su bayyana mahangarsu dangane da hanyoyin da ya kamata a kyautata lamarin fatawa ta hanyoyi na zamani, domin musulmi su amfana da hakan cikin sauki a duk inda suke a duniya.
Baya ga haka kuma a zaman za a tattauna hanyoyin da suka dace domin fitar da fatawoyi da suke a kan hanya, domin yi wa matasa saiti wadanda akan yaudare su tare da saka su cikin ayyukan ta’addanci da sunan addini.