An fara gwanjon rigar da Diego Maradona ya sanya a lokacin da ya zura kwallaye biyu a ragar Ingila, cikinsu har da wadda yayi amfani da hannu wajen zura ta, a yayin gasar kofin duniya ta shekarar 1986.
Za a cigaba da wannan gwanjo har zuwa ranar 4 ga watan Mayu mai zuwa.
Rigar dai a yanzu mallakin tsohon dan wasan tsakiya ce na Ingila Steve Hodge, wanda ya yi musayar ta da Maradona bayan da Argentina ta doke su da ci 2-1.
A kimanin shekaru biyu da suka gabata, bayan mutuwar Maradona a 2020, Hodge ya ce rigar gwarzon dan wasan ba ta siyarwa ba ce.
A wani labarin na daban Arsenal ta sake farfado da fatanta na kammala gasar Firimiya ta bana a tsakanin kungiyoyi hudu na farko , abinda zai ba ta damar halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta badi, bayan doke Chelsea da kwallaye 4-2 har gida.
Nketiah mai shekaru 22 ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea kafin daga bisani Timo Werner ya rama, Emile Smith Rowe ya sake ci wa Arsenal kwallo ta biyu, nan da nan kuma Cesar Azpilicueta ya sake ramawa Chelsea.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Nketiah ya sake cin kwallonsa ta biyu, ta amma ta uku ga Arsenal, sannan Bukayo Saka ya ci ta hudu.
Yanzu haka Arsenal tana matsayi na biyar a gasar Firimiya, bayan Tottenham ta hudu, dukkaninsu da 57-57, sai dai banbancin kwallaye, yayin da ya rage sauran wasanni shida a karkare kakar wasa ta bana.
A halin yanzu kuma maki 5 ne kawai tsakanin Arsenal da Chelsea wadad ke matsayi na uku da maki 62.
A wasu daga cikin wasannin da aka buga a jiya, Manchester City ta lallasa Brighton da kwallaye 3-0, an kuma tashi 1-1 tsakanin Everton da Leicester City.