Manzon Musamman Ta MDD, Ta Gana Da Masu Rikicin Shugabanci A Libiya.
Manzon musamman ta Majalisar Dinklin Duniya, kan rikicin Libiya, ta yi wata ganawa da shugabannin dake gabad a juna a kasar.
Mme Stephanie Williams, ta yi kira ga dukkan bangarorin dasu kai zuciya nesa domin shinfida zaman lafiya a kasar.
Libiya ta sake fadawa cikin rudani ne bayan da a karshen makon jiya ta tsinci kanta da firaministoci guda biyu dake ikirarin shugabancin gwamnatin Tripoli, lamarin da ya kara jefa kasar cikin rikicin shugabanci da rarrabuwar kai.
Hakan ya zo ne bayan da majalisar dokokin kasar ta nada Fathi Bachagha, domin maye gurbin Abdelhamid Dbeibah, wanda shi kuwa ya ce ba zai mika mulki ba saiga gwamnatin da aka zaba.
MDD, dai ta bakin manzon ta, ta bukaci bangarorin dasu maida hankali wajen shirya zabukan kasar da zasu kunshi kowa da kowa a cikin gajeren lokaci.
A watan Disamba bara ne ya kamat Libiya ta shirya zaben shugaban kasar saidai hakan bai yiwu ba.