Manyan kasashen duniya na taro a Berlin na kasar Jamus domin lalubu hanyoyin samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar Libya, ta yadda zata tsaya da kafafunta wajen samun gudanar da zaben a ranar 24 ga watan Disamba.
Taron wanda Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi ya samu halartar Firayiministan gwamnatin rikon kwartar Libya Abdul Hamid Dbeibah da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da kuma ministocin harkokin wajen Faransa da Turkiya da kuma Masar.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov bai halarci taron ba, amma Mataimakin sa Sergey Vershinin ya wakilce shi.
Wannan dai shine taro karo na biyu dake gudana a Berlin a Kokarin manyan kasashen duniya na kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe sama da shekaru goma ana gwabzawa a kasar Libya.
Bayan wanda aka gudanar a shakarar 2020, kafin annobar korona, wanda shugabannin kasashen Turkiya da Rasha da Faransa suka.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinkin, ya bukaci janye sojojin kasashen waje dake cikin kasar dake fama da rikici a Arewacin Afirka.
Kasar liniya dai ta shiga yanayin tashin hankali da rashin tsaro tun lokacin da amurka da sauran manyan kasashen duniya suka kifar da gwamnatin muhammad gaddafi kuma zuwa yau dinnan ba’a samu kwanciyar hankali ba.
Al’ummar kasar libiya sun fada cikin tashin hankali da barazanar tsaro sakamakon shigowar sojojin amurka da sauran kasashen duniya, inda libiya ta zama matattarar rashin tsaro da tashe tashen hankula.
Shigowar kasar amurka ya bada kofar tabarbarewar tsaro kuma an rasa samun tsayayyiyar gwamnati wacce zata tabbatar da tsaro da jin dadin al’ummmar kasar ta libiya.