Kafar sadarwa ta Press Tv ta rawaito cewa, manyan wakilai daga harkar Hamas na ziyara a kasar Saudiyya sakamakon bukatar da bangarorin biyu sukayi na gyara alaka.
Kamar yadda Press Tv ta tabbatar, kafar sadarwa ta Palestine ta tabbatar da cewa manyan wakilan na Hamas sun isa birnin Jeddah ranar litinin.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, wakilan zasu gabatar da umara a karshen azumin watan ramadana.
Alaka tsakanin Riyadh da Hamas ta lalace tun shekarar 2007 bayan Hamas din ta samu nasara a zaben majalisar kuma ta ci karo da jam’iyyar siyasa ta Fatah a zirin gaza.
A shekarar 2019 Saudiyya ta kama gomomin mambobin Hamas bisa zargin suna barazana ga masarautar.
A ‘yan watannin da suka gabata shugabannin Hamas sun aike da sakonni da suke nuna kyautatatuwar alaka tsakanin su da Saudiyyan, a nata bangaren Saudiyya ta saki wasu mambobin Hamas din ciki har da Mohammad Al-Khudari.
Biyo bayan sakin Flasdinawa biyu wadanda ke da alaka da Hamas a watan february, kungiyar Hamas ta bayyana fatan wanna cigaban zai zama shere fagen bude sabon shafi da ‘yan uwa a Saudiyya.
“Muna tabbatar da sha’awar mu kan kyakykyawar alaka da ‘yan uwan mu na Saudiyya da kuma duk sauran ‘yan uwan mu a kasashe domin hidima ga Palestine, larabawa da kuma da kuma gwamnatin musulunci” kamar yadda yazo a bayanin.
Ziyarar manayan wakilan Hamasa na zuwa ne bayan wata guda da yarjejeniyar Iran da Saudiyya bisa shiga tsakanin China, inda kasashen suka yarda su dawo da alakar diflomasiyya.
Dai dai da ziyarar wakilan Hamas zuwa Saudiyyan, shuagban kasar Palestine yana ziyara a Saudiyya sakamakon gayyatar da aka masa.
A tsammanin zai gana da Muhammad bn Salman a ranar talata kuma zasu tattauna batu sabbin cigaban da aka samu a Palestine da kuma yanayin nahiya, sa’annan kuma da kyautata alaka tsakanin Palestine da Saudiyya kamara yadda Wafa News Agency suka rawaito