Tawagar kwallon kafa ta Young Boys ta yi nasarar lallasa Manchester United duk da kwallo guda da Cristiano Ronaldo ya zura mintuna 13 da fara wasa.
Sauyin da Ole Gunnar Solskjear ya yi a minti na 95 ta hanyar cire Cristiano Ronaldo da Bruno Farnandes ya baiwa Young Boys damar zura kwallonta na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu bayan kuskuren Jesse Lingard da ya maye gurbin Ronaldo.
Wasan na jiya shi ne irinsa na 177 da Ronaldo ya buga karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.
Bugu da kari kwallon Ronaldo mai shekaru 36 ita ce ta 3 da ya zurawa sabuwar kungiyar tasa tun baya kulla kwantiragi da ita a watan jiya.
Wasa na gaba da United za ta doka shi ne tsakanin ta da Villarreal ranar 29 ga watan nan.
A wasannin na jiya dai karkashin rukunin na F Villarreal ta yi canjaras ne da Atalanta da kwallaye 2 da 2 kungiyoyin da dukkaninsu ke dakon haduwarsu da United a nan gaba.
A wani labarin mai kama da wannan ungiyar Manchester United ta bada tabbacin cewa Cristiano Ronaldo zai sake sanya riga mai lamba 7 bayan komen da yayi mata, shekaru 12 bayan sauyin shekarar da yayi daga Kulob din a karon farko.
A waccan lokacin, Ronaldo ya ci wa United kwallaye 118 a wasanni 292 da ya buga mata, tare da taimaka mata wajen lashe kofuna tara, ciki har da na gasar Firimiya uku da na Zakarun Turai daya.
A baya bayan nan ne dai Angel Di Maria ya caccaki Manchester United kan yadda kungiyar ta ke baiwa riga mai lamba 7 matsayi na musamman.
Dan wasan na Argentina ya ce bai taba damuwa da gadon rigar mai lamba bakwai a Manchester United ba, a lokacin da ya koma kungiyar.