Magoya bayan Manchester United da kuma wasu masu sharhi kan kwallon kafa, sun caccaki matakin da Solskjaer ya dauka yayin wasan, inda ya maye gurbin Jadon Sancho da Diogo Dalot, bayan da aka kori Aaron Wan-Bissaka saboda jan kati
Rahotanni kamar yadda jaridar UK Mirrow ta ruwaito na cewa, ana sa ran United ta tantance wanda za ta kulla yarjejeniya da shi, tsakanin Antonio Conte, Zinedine Zidane da Brendan Rodgers.
Conte da Zidane dai a yanzu haka babu wata kungiya da suke horaswa, bayan rabuwa da Inter Milan da Real Madrid, yayin da Rodgers ke jagorantar Leicester City.
Sauyin da Ole Gunnar Solskjear ya yi a minti na 95 ta hanyar cire Cristiano Ronaldo da Bruno Farnandes ya baiwa Young Boys damar zura kwallonta na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu bayan kuskuren Jesse Lingard da ya maye gurbin Ronaldo.
Wasan na jiya shi ne irinsa na 177 da Ronaldo ya buga karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.
Bugu da kari kwallon Ronaldo mai shekaru 36 ita ce ta 3 da ya zurawa sabuwar kungiyar tasa tun baya kulla kwantiragi da ita a watan jiya.
Wasa na gaba da United za ta doka shi ne tsakanin ta da Villarreal ranar 29 ga watan nan.
A wasannin na jiya dai karkashin rukunin na F Villarreal ta yi canjaras ne da Atalanta da kwallaye 2 da 2 kungiyoyin da dukkaninsu ke dakon haduwarsu da United a nan gaba.