Manchester City ta lashe kofin gasar Premier na bana kuma na takwas a jumlace, bayan doke Aston Villa 3-2 a Etihad ranar Lahadi.
City ta kammala gasar da maki 93 daya tsakaninta da liverpool mai biye mata da maki 92, Chelsea ke na uku da maki 74, sai Tottenham a matsayi na hudu da maki 71.
PSG
Tun kafin wannan lokaci Paris Sint Germain ta lashe Gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, bayan da ta tashi 1-1 da RC Lens a wasan mako na 34 cikin watan Afrilu, yanzu haka ta karkare gasar da maki 86, yayin da Marseille ta zo na biyu da maki 71, sai monaco da maki 69 sannan Rennes da maki 66.
Mbappe
Tuni dan wasan PSG Kylian Mbappe ya watsawa Madrid kasa a ido bayan yanke shawarar ci gaba da zama a kungiyar dake taka leda a gasar Ligue 1.
Madrid
Itama Real Madrid ta lashe gasar La Liga karo na 35 tun kafin karkare gasar.
Madrid ta karkare kakar bana da maki 86, Barcelona ken a biyu na maki 73, sai Atletico ken a uku da maki 71 sai kuma Sevilla da maki 70 amatsayi na 4.
A wani labarin na daban manajan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya yi ikirarin cewa har yanzu bai karaya da cewa kungiyar tasa za ta iya dara takwararta Manchester City tare da dage kofin firimiya a bana ba.
A cewar Klopp ya na da kwarin gwiwar cewa Liverpool cikin wannan kaka za ta kafa tarihin dage kofuna 3 ko fiye ciki kuwa har da na firimiya da kuma zakarun Turai da ta samu damar zuwa wasan karshe.
City ta tsawaita tazarar da ke tsakaninta da Liverpool daga maki 1 zuwa 3 bayan lallasa Newcastle da kwallaye 5 da nema wanda ya bata damar zarta ta hatta da yawan kwallaye kwana guda bayan Reds ta yi canjaras da Tottenham da kwallo 1 da 1.
Jurgen Klopp ya bayyana cewa duk da yana fatan shigewa gaban City don lashe kofin firimiya hakan bazai hana shi tattala ‘yan wasansa don tunkarar wasannin karshe na cin kofin FA tsakaninsu da Chelsea a asabar din nan mai zuwa ba da kuma wasan karshe na cin kofin zakarun turai ranar 28 ga wata tsakaninsu da Real Madrid.
A cewar Klopp idan har ba a kai ga wasan karshe ba Liverpool ba za ta cire rai kan yiwuwar dage kofin ba, kalaman da ke zuwa dai dai lokacin da Pep Guardiola na Manchester City ke ikirarin cewa ilahirin Ingila na goyon bayan Liverpool ne don ganin ta lashe firimiya.