Manazarta Masar: Isra’ila ta damu matuka game da komawar alakar Iran da Masar
Ayman Salameh mamba a majalisar kula da harkokin wajen kasar Masar a wata hira da yayi da jaridar Al-Arabi Al-Jadiid, ya dauki gwamnatin yahudawan sahyoniya a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas wajen daidaita alaka tsakanin Tehran da Alkahira.
Daidaita da maido da huldar diflomasiyya tsakanin Masar da Iran ba abu ne mai sauki ba saboda akwai cikas da kalubale, wadanda mafi muhimmancinsu su ne: bambance-bambancen siyasa da na tsaro.
Mamban majalisar kula da harkokin wajen Masar ya kara da cewa: Alkahira da Tehran suna da ra’ayi daban-daban kan batutuwan siyasa da tsaro na yankin, kamar batun Falastinu da halin da ake ciki a Siriya, Yeman da Iraqi.
“Dukkanin Masar da Iran suna neman karfafa tasirin yankinsu. Akwai rikici kan tasirin yankin saboda kasashen Masar da Iran suna neman fadada tasirinsu a yankin kuma wannan batu na iya haifar da rikici tsakanin kasashen biyu a wasu yankuna kamar yankin Gulf na [Fara].
A sa’i daya kuma, Salameh ya yi ishara da cewa: Daya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas a kan hanyar daidaita huldar da ke tsakaninsu shi ne tsoron da Isra’ila ke da shi na komawar dangantakar diflomasiyya tsakanin Masar da Iran. Isra’ila ta yi imanin cewa wannan mataki zai fadada tasirin Iran a yankin.
Sai dai ya ce: Amma duk da haka, ci gaban da aka samu a yankin baya-bayan nan, kamar komawar dangantakar diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya, ya haifar da samar da kyakkyawan yanayi na maido da huldar jakadanci tsakanin Iran da Masar.
A kwanakin baya ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hossein Amirabdollahian ya gana da takwaransa na Masar Sameh Shukri a gefen taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya.
“Nasser Kanani” mai magana da yawun ma’aikatar diflomasiyya ta Iran, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da wannan taro, ya bayyana wannan taron a matsayin mai kyau da kuma wani sabon ci gaba.