Mamayar Ukraine Shin Putin zai harba makaman nukiliya?
Bari na fara da fadin wani abu. Na sha cewa: “Putin ba zai taba yin abu kaza ba.” Amma sai na ji ya yi abin.
“Na yi imani ba zai taba kwace yankin Crimea ba, ko?” Amma ya yi haka.
“Ba zai taba kai hari a yankin Donbas ba.” Sai kawai naji ya yi.
“Na san ba zai taba kai hari gadan-gadan ba a Ukraine.” Sai ga shi ya kai harin.
Na saka kalmomin “ba zai taba” ba cikin abubuwan da ba su shafi Vladimir Putin ba samsam.
Wannan ne ya sa na yi wannan tambayar:
“Ba zai taba zama shugaba na farko da zai harba makaman nukiliya ba. Ko?”
Wannan ba irin tambayar da malaman jami’a ke yi wa dalibansu ba ce. Ba a jima ba da shugaban na Rasha ya bukaci dakarun kasar masu kula da makaman nukiliya da su zama cikin shiri, saboda abin da ya kira “kalaman tsokana” da shugabannin kasashen da ke kungiyar tsaro ta Nato ke furtawa.
Abin da ya kamata mu yi shi ne: A saurara da kyau domin a fahimci abin da Putin ke cewa. Ranar Alhamis da ta gabata ita ce ranar da ya sanar zai tura sojojin kasar zuwa Ukraine, kuma ya yi wani gargadi mai ban tsoro:
“Duk wanda ke tunanin yin katsalandan daga waje, to za kai fuskanci sakamakon da ya zarce duk wanda wani cikinku ya taba fuskanta a tarihi.”
“Kalaman na Putin sun yi kama da kashedin kai harin nukiliya,” in ji Dmitry Muratov, wanda ya taba lashe lambar Yabo ta Nobel kan zaman lafiya, kuma shi ne editan jaridar Novaya Gazeta.
“A cikin wannan jawabin nasa, Putin bai taka rawar shugaban kasar Rasha ba, ya taka rawar shugaban duniyarmu ne baki daya; kamar yadda wanda ya sayo sabuwar mota ke nuna wa jama’a makullinta ta hanyar jujjuya shi a yatsansa. Putin na jujjuya kusar harba makaman nukiliya ne. Ya sha cewa: Idan babu Rasha, me zai sa wannan duniyar ta ci gaba da kasancewa? Babu wanda ya mayar da hankalinsa kan kalaman nasa. Amma wannan barazana ce da ke cewa idan ba a yi ma Rasha abin da ta ke so ba, to za a ruguza komai.”
A wani fim da aka hada a 2018, Shugaba Putin ya yi tsokacin da ke cewa “…idan wani ya yanke shawarar ruguza Rasha, muna da damar mayar da martani. Lallai zai zama babban koma-baya ga dan Adam da kuma duniya. Amma ni dan Rasha ne kuma shugabanta ne ni. Me zai sa mu so wannan duniyar idan babu Rasha a cikinta?”
A shekarar 2022, Putin ya kai hari kan Ukraine, sai dai sojojin kasar na nuna turjiya: Kasashen Yammacin Turai sun hada kansu wuri guda, kuma sun dauki matakan da ka iya illata tattalin arzikin Rasha.
“An saka Putin a wani wuri mai matukar wahala,” in ji Pavel Felgenhauer. “Ba shi da sauran matakan da zai iya dauka idan kasashen yammacin Turai suka hana babban bankin Rasha ci gaba da hada-hada da sauran kasashen Turai”.
“Cikin martanin da zai iya dauka akwai na hana kasashen Turai amfana da iskar gas din da Rasha ke sayar musu. Wani martanin kuma shi ne a tayar da bam din nukiliya cikin teku tsakanin Birtaniya da Denmark.”
Idan ya zabi daukan mataki na biyu – wato harba makaman nukiliya – akwai wani cikin makusantarsa da zai iya hana shi?
“Babu wanda zai iya tunkarar Putin,” in ji Pavel Felgenhauer. “Mun fada wani rami mai matukar zurfi da hatsari.”
Yakin na Ukraine, yakin Vladimir Putin ne. Idan ya cimma bukatunsa na soji, makomar Ukraine ta kasa mai cikakken ‘yanci zai zama abu mai wuya. Idan aka ga kamar yana gazawa, kuma yana shan kaye a fagen yaki, abin fargaba a nan shi ne Fadar Kremlin na iya daukan wasu matakai masu ban tsoro.
Musamman ma idan kalaman “ba zai taba yin haka ba” sun zama tsohon al’amari.