Mali ta samu karin makaman soji daga Rasha.
Karin jiragen helikwafta na yaki biyu da Mali ta saya a hannun Rasha da na leken asiri sun isa kasar, bayan Tarayyar Turai ta dakatar da horon da take bai wa sojoji a yankin Sahel.
Wata sanarwa da gwamnatin Mali ta fitar, dauke da sa hannun babban hafsan sojin kasar, Manjo Janar Oumar Diarra, ne ya tabbatar da karbar jiragen yakin.
Fadar gwamnatin Mali ta fitar da wani bidiyo, inda a ciki ake ganin lokacin da jirgin dakon kaya na Rasha ya ke sauye kayana filin jirgin sama na Bamako.
Mr Diarra ya yaba wa taimakon na Rasha ga kasarsa, inda ya jaddada dangantaka na kara yauki tsakanin kasashen biyu.
A watan da ya gabata ne dai, Mali ta fara karbar jiragen yaki kashin farko da ta saya daga Rasha, jim kadan bayan ziyarar da ministan tsaro da hafsan sojin sama na kasar sun dawo daga Rasha.
Kafar yada labaran Mali ta yi ta yada batun saya da kawo jiragen yakin daga Rashar. Ma’aikatar tsaron kasar ta kare matakin alakarta da Rasha, da batun cinikin makaman daga kamfanin Wagner mai cike da ce-ce-ku-ce.
Kasashen da dama sun yanke alaka da Rasha kan mamayar da ta yi da kaddamar da yaki a Ukraine.