Wani jirgin saman daukar kaya ya isa Mali da jirage masu saukar ungulu 4 da wasu makamai daga Rasha, kamar yadda ministan tsaron kasar, Sadio Camara ya bayyana.
Wadannan kayayyaki sun isa Mali ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasar da Faransa, wadda ke taimaka mata wajen yakar ta’addanci ke ci gaba da yin tsami, bisa rahotanin cewa Mali na shirin daukar sojojin haya daga Rasha.
A wani labarin na daban mai kama da wannan ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce tabbas mahukuntan kasar Mali sun fara tuntubar kamfanonin sojin haya masu zaman kansu da ke Rasha don magance matsalar rashin tsaro da kasar ke fama da ita yau kusan shekaru 9.
A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Rashar ya tabbatar da cewa magana ta fara nisa tsakanin kamfanin na Wagner da mahukuntan Mali kasar da ke karkashin mulkin Soja a yanzu haka kuma ta ke fama da matsalolin tsaro.
Wasu bayanai sun ce Sojin hayar na Wagner za su taimakawa Mali magance matsalar tsaron baya ga horar da Sojinta a cikin kasar.
Tuni dai kasashen Duniya suka fara gargadin Malin game da daukar Sojin hayar na Wagner ‘yan Rasha, sai dai gwamnatin Sojin kasar ta yi watsi da kiraye-kirayen duk da cewa da farko ta musanta batun.
A bangare guda Faransa wadda ke matsayin uwar goyon Malin ta gargadi Rasha akan yiwa kasar ta yankin Sahel katsalandan a harkokinta na cikin gida.