Mali; Masu Zanga-Zanga Sun Bai Wa Sojojin Faransa Na “Barkhan” Sa’o’i 72 Da Su Fice.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayar da rahoton cewa, mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga a birnin Gao, wanda shi ne tunga ta karshe ta Faransawa a kasar Mali, domin nuna adawa da ci gaba da kasancewar dakarun “Barkhan” na Faransa, yayin da masu zanga-zangar suka ba sojojin na Faransa wa’adin sa’o’i 72 da su fice.
Masu zanga-zangar sun bayyana kansu a matsayin masu rajin kare kasarsu daga hankoron mulkin mallakar Faransa kan kasarsu, a kan suka bukaci sojojin Faransa da su fice a cikin wa’adin kwanaki uku daga jiya Lahadi 14 ga watan Agusta.
A cikin watannin baya-bayan nan ne dai tabarbarewar dangantaka ta kara yin kamari tsakanin majalisar soji da ke mulki a Bamako da kuma Faransa wadda ta yi wa Mali mulkin mallaka.
READ MORE : Abdollahian; Iran Ba Za Ta Yi Kasa A Gwiwa Wajen Kare Hakkokinta Ba.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nuna hotunan masu zanga-zangar suna dauke da kwalaye da aka yi rubutu kansu, da ke neman sojojin Faransa su fice ba tare da bata lokaci ba, yayin da kuma wasu kwalayena aka rubuta babu sauran mulkin mallaka a kan kasar Mali.