Mali; Gwamnatin Ta Tabbatar Da Cewa Yan Ta’adda Sun Kai Hari Kan Barikin Sojojin Kati.
Gwamnaton sojoji a kasar Mali ta tabbatar da cewa yan ta’adda sun kai hare-hare kan barikin Kati barikin soje mafi girma a kasar a ranar jumma’an da ta gabata.
Shafin yanar gizo na ‘AfricaNews’ ya nakalto wani bayani wanda gwamnatin sojojin ta fitar inda take cewa, yan ta’adda sun kai hare-hare kan barikin, amma sojojin sun maida martani, kuma sun sami nasarar kashe yan ta’adda 7 a yayinsa suka kama wasu wasu 8 da ransu.
Labarin ya kara da cewa sojojin kasar sun kama wani a kusa da inda aka kai harin dauke da bindiga da cike da harsasai sannan wani kuma yana dauke da katunan shaida na mutane da dama a tare da shi inji Cheikh Coulibaly wani mazaunin garin Kati.
READ MORE : Iran Tana Fitar Da Kayakin Lantarki Da Injuna Zuwa Kasar Rasha Don Kasuwanci.
Tun shekara ta 2012 ne gwamnatin Mali take yakar yan ta’adda wadanda suke kokarin kifar da gwamnatin kasar don aiwatar da abinda suke kira daular musulunci.
READ MORE : General na Sahayoniya; sansanonin sojojin saman Isra’ila za su gurgunta a yakin da ke tafe.
READ MORE : Yan Majalisar Faransa Sun sanya Hannun Kan Daftarin Kudurin Yin Tir Da Laifin Yakin HKI Kan Falasdinu.