Mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Chilima ya rasu sakamakon hatsarin jirgin da ke dauke da shi ya yi a ranar Litinin.
Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chikwera ya ce “jirgin nasa ya daki dutse” ne inda jirgin ya tarwatse kuma mista Chilima da duka wadanda ke cikin jirgin suka rasu.
An dai samu tarkacen jirgin ne a kusa da wani tsauni.
An dai kwashe awanni ana bincike domin gano jirgin saman da ke dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi.
A ranar Litinin ne, wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, ta bayyana cewar an daina jin duriyar jirgin saman mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi bayan da ya bar babbar birnin kasar, lilonge, a ranar Litinin da safe.
Shugaban kasar ya bayar da umarnin gudanar da aikin ceto bayan da jami’an sufurin jiragen sama suka gaza jin duriyar jirgin.
Kamata ya yi jirgin ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Mzuzu, da ke shiyyar arewacin kasar da misalin karfe 10 na safe.
Bayan da aka sanar da shi game da afkuwar lamarin, nan take shugaban kasar Lazarus Chakwera ya soke tafiyar da ya shirya yi zuwa tsibirin Bahamas.
A wani labarin na daban bata gari sun tare hanyar Kano daga Maiduguri, wani fasinja da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce shi da wasu fasinjoji sun shafe sa’o’i a tsaye kafin su wuce.
“Muna kan hanyar zuwa Kano daga Maiduguri lokacin da direbanmu ya samu labarin an tare hanyar,” in ji shi.
DUBA NAN: Kaso 70 Cikin Dari Na Yaran Najeriya Basa Gane Abinda Ake Koya Musu
“Mun dade muna jiran sojoji su bude hanya amma ba mu san yaushe za su zo ba. Muna tsaye a nan.”