Malamin Hindu da ke iƙirarin sanin abin da ke cikin zukatan mutane
Ƙasar Indiya na daga cikin kasashen da suke da yawan addinai, amma wani sabon mabiyin addini da ya ɓullo a kwanan nan da ake kira “godman” , wanda ke ta janyo ce-ce-ku-ce sama da makonni biyu da suka gabata a kasar.
Magoya baya Dhirendra Krishna Shastri, wanda aka fi sani da Bageshwar Dham Sarkar sun ce yana da wani irin abu na ubangijinsu da yake amfani da shi wajen warkar da marasa lafiya.
Sun ce yana warkar da waɗanda aljanu suka shafa da kuma taimaka wa ‘yan kasuwa da suke fama da matsalar kuɗaɗe.
Fadan mai shekara 26 da ke jagorantar wajen bauta na Bageshwar Dham, a birnin Madhya Pradesh da ke tsakiyar India, yana sanya kaya cikin mabambantan launuka.
Matashin malamin ya zama abin tattaunawa a gidan talabijin da kafafen sada zumunta a kasar.
A ‘yan makonnin nan, wata tashar India da ke watsa labarai da harshen Hindu ta bai wa malamin daruruwan awanni domin nuna irin ƙarfin baiwar da yake da ita.
Kuma maudu’an da yake tattaunawa a kansu masu alaƙa da addini kamar su auren mabiya mabambantan addinai, na yawan janyo kanun labarai a ƙasar.
Mabiyansa a kafafen sada zumunta sun ƙara yawa zuwa miliyan bakwai da rabi – a Facebook su miliyan 3.9 a Youtube sun kai dubu 300 a Instagram sai 72,000 a Twitter.
Wasu daga cikin shahararrun bidiyoyinsa an kalle su tsakanin miliyan uku zuwa miliyan 10.
Sunansa ya ƙara fitowa ne a watan Janairu, bayan wasu tambayoyi da aka riƙa yi masa kan cewa yana da ikon warkar da marasa lafiya, tare da sanin abun da ke cikin zukatan mutane.
Wata ƙungiya da ake kira Andhashraddha Nirmoolan Samiti, ta sanya kyautar rupee miliyan uku daidai da dala 36,500, idan Mista Shastri ya faɗi abin da ke zuciyar mutane 10 da ya ga dama.
An yi wannan ƙalubale ne lokacin da Mista Shastri ya sauka a birnin Nagpur a Maharashtra – inda Mista Manav yake zaune.
Lokacin da Mista Shastri ya bar garin ba tare da cewa uffan ba game da wannan ƙalubale sai wasu suka riƙa cewa ya tsere ne domin ba zai iya ba.
Tun daga nan, yake tattaunawa da gidajen talbijin inda yake yawan musanta cewa ya guje wa wannan ƙalubale ne.
Yana kuma cewa a shirye yake ya ɗauki wannan ƙalubale, amma ba a Maharashtra ba.
Maimakon haka, ya nemi a yi mahawarar a jihar Chhattisgarh mai makwaɓataka, inda ba gidan kowa ba ne.
Amma Mista Manav yace tun da ya yi iƙirarin ikon da yake da shi a Maharashtra to dole ne ya tabbatar da iƙirarinsa a jihar.
Tun lokacin da aka fara wannan turka-turka, rahotanni ke cewa Mista Manav ya riƙa fuskantar barazanar mutuwa kuma tun daga nan ‘yan sanda suke ƙara matsa lamba kan harkokin tsaronsa.
A kwanakin baya, Shi ma Mista Shastri ya shigar da ƙara wajen ‘yan sanda kan cewa shi ma ana yi masa barazanar kisa ta waya.
Wannan muhawara ta karaɗe duka kafafen yaɗa labarai – har da wani mai rahoto da aka taɓa nuna wa yana taba kafarsa tare da magana kan yadda yake warkar da mutane da kuma ikon da yake da shi na karantar zukatan al’umma – hakan kuma ya ƙara masa shahara.
A wani taro da yaje, ya kira wani mutum da ake kira “Mukesh, wanda ke sanye da wata ƙaramar riga daga cikin taro.
Lokacin da mutumin ya hau kan dandamalin, ya ɗauki takarda ya rubuta duka matsalolin da suke damun iyalan Mukesh.
Bayan karanto matsalolin da suke damun shi kawai sai ya miƙa wuya.
Wani abu da ya faru mai kama da wannan shi ne, ya ƙara rubuta wa wata mahaifiya matsalolin da yaronta ke fuskanta masu kama da taɓin ƙwaƙwalwa.
“Ta riƙa karantawa” wanda ya ce hakan zai taimaka wajen kawo waraka ga yaron da kuma matsalar kuɗi da suke ciki,” kamar yadda ya shaida mata.
Irin waɗannan abubuwa da ya riƙa yi ya janyo masa aminci a zukatan mutane, ana kiransa “ɗan baiwa”.
Yayin da magoya bayansa ke iƙirarin yana da idanu uku, zai iya leƙa abin da ke zuciyarka da ranka.
Amma masu sukarsa na zarginsa da amfani da maita yana ruɗar magoya bayansa da ba su san komai ba.
Masu tsafi da masu duba a ƙasar sun yi taro kan cewa su ma za su iya duk wani abu da yake yi, suna cewa kawai rufa ido ne ba wani abu mai kama da baiwa a lamuransa.
Mista Shastri ya ce “ana ta sukarsa kan abubuwan da yake ana cewa ƙarya ce yake yi” amma ya ce yana da ikon samar da mafita ga duk wata matsala ta duniya”.
An samu wasu fitattun mabiya addinin Hindu da shugabanninsu da suka sha sanya ayar tambaya kan abubuwan da yake yi.
Suna cewa idan har zai iya yin wani abu na baiwa, to ya kamata ya gyara gidajen da suka rushe da waɗanda suka nutse a yankin Himalaya.
Mista Shastri ya saba bayyana kansa a matsayin haifaffen ƙasar kuma shi bai yi karatu ba, kamar yadda shafin wurin bautarsa ya wallafa a bayanan intanet.
Cewa tun yana yaro yana da sha’awar abubuwan da suka shafi addini, wani lokacin har barin makaranta yake ya tafi bauta.
An haife shi a 1996 a wani gari da ake kira Gada a lardin Chhatarpur, iyayensa ba masu hali ba ne sosai.
Ya daina zuwa makaranta domin neman abin da zai riƙa taimakon mahaifansa da shi.
Wani ɗan ajinsu ya shaida wa BBC cewa shekarun da suka gabata, Mista Shastri ya yi ɓatan dabo na kusan shekara guda.
Bayan wani lokaci kawai sai aka ga ya bayyana, ‘yan sisaya da masu faɗa a ji na ziyartar inda yake jagorantar bauta.
“Shekaru biyar gabanin nan, yana yawo ne a babur,” in ji abokin nasa.
A yau, yana yawo ne da jerin gwanon motoci da jiragen sama da ke binsa a wani lokacin a jirgi mai saukar ungulu a cikin India da wajenta.