Majalisar Malaman ta Falasdinu ta yi gargadi game da matakin da yahudawan sahyuniya suka dauka na gudanar da bukukuwan sadaukarwa a cikin masallacin Al-Aqsa a lokacin bukukuwan Idin yahudawa tare da neman halartar musulmi a cikin masallacin.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ya habarta cewa, Majalisar Malamai ta Falasdinu ta neman dukkanin musulmi da su kare masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus, Majalisar Malamai ta Falasdinu ta yi gargadi game da yunkurin yahudawan sahyoniya masu tsattsauran ra’ayi kan yunkurinsu na gudanar da bukukuwan yagudawa a cikin wannan masallaci mai alfarma.
A wani taron manema labarai da ta gudanar a Gaza, Majalisar Malamai ta Falasdinu ta sanar da cewa, wadannan kokarin na nufin kalubalantar ra’ayin musulmi tare da yin gargadin cewa yakin addini na iya fuskantowa nan gaba. Wannan majalissar ta bukaci halartar masallacin Al-Aqsa domin kare shi.
Muhammad Salem dan majalisar malamai na Palasdinawa ya bayyana cewa: Muna gayyatar Palasdinawa a birnin Quds da yankunan da aka mamaye a shekara ta 1948 da kuma yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, da kuma duk wanda zai iya isa masallacin Al-Aqsa da su yi duk abin da za su iya don halartar wannan masallaci da yin I’itikafi da ibada a cikinsa domin karya shirin azzaluman makiya. Taimakon Masallacin Al-Aqsa wajibi ne na addini ga duk wanda yake da ikon taimakawa.