Rahotanni daga babban birnin jamhuriyar musulunci na Iran na tabbatar da cewa a gobe laraba ake sa ran za’a gudanar da taron tunawa da shahadar Imam Ridha (S.a), kuma ana sa ran jagoran ‘yan uwa musulmi na najeriya Malam Ibrahim Yaqoob Al-zakzaky ne zai jawabin bude taron.
Malam zakzaky wanda bai jima da fitowa daga gidan kurkuku ba ya dingi ganawa da bangarori daban daban kama daga manyan almajiran sa, ‘yan uwan sa na jini zuwa kan iyalan shahidai wadanda aka kashe musu ‘yan uwa a dalilin gwagwarmaya.
Hirar karshe dai da malam zakzaky yayi itace wacce yayi da gidan talbijin na Press T.v inda ya tattauna muhimman batutuwa ciki kuwa har da batutuwan da suka shafi halin kunci da rashin tsaro da ake ciki a najeriya da kuma makomar kasar a mahangar shehin malamin.
Koma dai menene rahotanni suna tabbatar mana da cewa shehin malamin ne aka gayyata domin gabatar jawabin bude taron ranar tunawa da shahadar Imamin mabiya mazahabar shi’a na takwas watau Imam Ali Bn Musa Arridha (S.a).
Jawabin wanda ake sa ran malam zakzaky zai gabatar da kafar sada zumunta ta ”Skype” kuma kai tsaye ana sa ran kafafen yada labarai irin su ”shabake khabar” ”shabakeh ufuq” da kuma ”shabakeh 3” zasu haska kaitsaye.
Ana dai sa ran jawabin budewar da shehinmalamin zai gabatar daga birnin abujan najeriya ta hanyar ”skype” zai iya daukan a kalla mintuna biyar kafin ya kammala kuma a cigaba da gudanar da taron kamar yadda aka saba duk shekara.
Sheikh zakzaky dai na zaman jiran fasfo dinsa na tafiya gami da na matar domin shillawa kasashen ketare neman lafiya amma hukumomi a najeriya sun hana kuma sun gaza sanar da dalilin hana shehin malamin fita kasashen ketare neman lafiya duba da cewa kotu ta wanke daga laifukan da ake zargin sa dasu kuma ta tabbatar mana da ‘yancin sa na walwala ciki kuma har da tafiya ketare domin neman magani kamar yadda kowanne dan kasa yake da wannan damar.