Majalisar wakilan Amurka ta kasa zaɓen shugaba bayan yunƙuri uku
Majalisar Wakilan Amurka ta ɗage zamanta cikin yamutsi bayan yunƙurin da ta yi har uku na zaɓen Kevin McCarthy na jam’iyyar Republican a matsayin shugaba, ya ci-tura.
Wannan shi ne karon farko a ƙarni ɗaya da aka kasa zaɓen a ƙuri’ar farko.
Dan majalisa McCarthy, daga California, ya kasa samun rinjayen yawan kuri’un da ake bukata, 218, bayan da ‘yan majalisa 28 na jam’iyyarsa ta Republican suka juya masa baya, inda suka gwammace su zaɓi Jim Jordan a maimakonsa.
Sai dai duk da haka Mista McCarthy ya ce zai ci gaba da takarar har sai ya yi nasara.
A baya shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar, saboda haka ake sa ran ya zama kakakin a yanzu bayan da ‘yan Republican ɗin suka karɓe rinjaye da majalisar a zaɓen rabin wa’adi na watan Nuwamba.
Amma kuma idan aka ci gaba da rigima a takarar, to hakan zai tilasta wa ‘yan majalisar su nemi wani ɗan takarar daban.
Tasirin wannan koma bayan shi ne babu wani aiki da majalisar za ta iya gabatarwa har sai ta naɗa kakakinta.
A majalisar dattawan ƙasar kuma, ‘yan jam’iyyar Democrat mai mulkin ƙasar ke da rinjaye, abin da ke nufin ba lalle ne mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta ci gaba da kaɗa kuri’arta ba a duk lokacin da wani batu da ke gaban majalisar ya gamu da cikas.
Saboda a yanzu ‘yan Democrat ɗin na da ƙarin ƙuri’a guda da suka samu a zaɓen watan Nuwamba da aka yi a faɗin ƙasar.