Majalisar Tarayyar Turai Na Kan Bakanta Na Shirin Gudanar Da Bincike Kan Manhajar Leken Asiri Ta Isra’ila.
Majalisar Tarayyar Turai na da niyyar amincewa da kafa wani kwamiti da zai binciki amfani da manhajar leken asiri ta Pegasus a Tarayyar Turai.
Kungiyar ‘Yan Jarida mai Zaman Kanta ta Duniya ta wallafa a shafinta na twitter cewa: “Muna maraba da matakin da Majalisar Tarayyar Turai ta dauka na amincewa da kafa kwamitocin bincike don gudanar da bincike kan amfani da manhajar leken asiri na Pegasus a cikin Tarayyar Turai, ciki har da a kan ‘yan jarida.”
Binciken hukumomin kasar Hungary bai wadatar ba kawo yanzu, yana da mahimmanci wannan binciken ya bayar da sakamako mai gamsarwa. A cewar kungiyar ‘yan jarida ta duniya.
Wani shafin twitter ya bayyana cewa: Zarge-zarge a cikin Tarayyar Turai cewa hukumar leken asirin Hungary ko kuma hukumar tsaron kasar ta yi amfani da manhajar leken asiri ta Pegasus wajen leken asiri kan ‘yan jarida.
Rashin iya sa ido kan fasahar leƙen asiri a cikin ƙungiyar tarayyar turai yana nufin cewa adadin ƙasashe mambobin da suka sayi fasahar NS ba su da tabbas.