Shugaban Majalisar Tarayyar Afirka Majalisar Tarayya Afirka ya soki Isra’ila kan kisan da ta yi wa Falasɗinawa masu jiran tallafi
Shugaban Majalisar Tarayyar Afirka Majalisar Tarayya Afirka ya soki Isra’ila kan kisan da ta yi wa Falasɗinawa masu jiran tallafi
Moussa Faki Mahamat ya zargi Isra’ila da “kisan Falasɗinawa masu yawa” a saƙon da ƙungiyar Tarayyar Afirka ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.
Faki Mahamat ya yi kira a gudanar da bincike na ƙasashen duniya kan kisan rashin imani da Isra’ila take yi wa Falasɗinawa. / Hoto: Reuters
Shugaban Majalisar Tarayyar Afirka Majalisar Tarayya Afirka ya soki Isra’ila kan kisan da ta yi wa Falasɗinawa fiye da ɗari ɗaya a wani hari da ta kai musu lokacin da suke jira a ba su tallafin kayan jinƙai.
Moussa Faki Mahamat ya zargi Isra’ila da “kisan Falasɗinawa masu yawa” a saƙon da ƙungiyar Tarayyar Afirka ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.
Ya yi kira a gudanar da bincike na ƙasashen duniya kan kisan rashin imani da Isra’ila take yi wa Falasɗinawa.
The African Union Commission Chairperson strongly condemns the mass killing of Palestinians queuing for humanitarian aid : https://t.co/VvRp2aBa0l pic.twitter.com/cr9VBoqPmH
— African Union (@_AfricanUnion) March 2, 2024
“Shugaban Majalisar Tarayyar Afirka H.E. Moussa Faki Mahamat ya yi tir da dakarun Isra’ila da kakkausar murya kan kisa da raunata Falasɗinawa sama da 100 waɗanda ke neman tallafin jinƙai domin tsira da rayuwarsu,” in ji sanarwar.
“Shugaban Majalisar Tarayyar Afirka ya yi kira a gudanar da bincike na ƙasashen duniya game da wannan batu sannan a hukunta waɗanda suka aikata laifi,” yana mai jaddada kira na “tsagaita wuta nan-take kuma ba tare da wasu sharuɗɗa ba”.
Ranar Alhamis ne dakarun Isra’ila suka buɗe wuta kan Falasɗinawa fararen-hula da ke ƙoƙarin karɓar kayan abinci na agaji a Birnin Gaza lamarin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum 100, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta yankin.
Hakan na faruwa ne a yayin da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi cewa: “Idan abubuwa ba su sauya ba, bala’in yunwa na dab da faɗa wa arewacin Gaza.”