Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce sojojin Mali sun hana dakarunsu sintiri a tsakiyar garin Djenne, yankin da ake fama da tashe-tashen hankula da kuma hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.
Wannan al’amari dai ya zo ne makwanni kalilan kafin muhawarar da Majalisar Dinkin Duniya za ta yi a kan ko za ta sabunta wa’adin aikinta na wanzar da zaman lafiya.
Wani mai magana da yawun rundunar Minusma, Olivier Salgado, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “Abin takaicin shi ne, yadda sojojin Mali suka hana ‘yan sandan Majalisar Dinkin Duniya yin sintiri da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin 16 ga watan Mayu, bisa hujjar cewa ana gudanar da ayyukan soji a yankin.
Sai dai Kanar Karim Traore, kwamandan sojojin Mali na shiyyar yankunan Mopti da Djenne, ya ce Mali ba ta kawo cikas ga ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ba, kuma an dage aikin sintirin da dakarun Majalisar Dinkin Duniya za su yi ne kawai, ba haramtawa ba, saboda ayyukan sojin da ke gudana.
A farkon wannan shekarar ne dai gwamnatin mulkin sojan kasar Mali ta kafa dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a wani babban yankin kasar lamarin da ya dagula ayyukan Majalisar Dinkin Duniya.
Har yanzu kuma rundunar majalisar ta Minusma na jiran izinin shiga garin Moura, a tsakiyar kasar ta Mali, inda kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce sojojin Mali da sojojin haya na Rasha sun kashe fararen hula 300 a watan Afrilu.
A wani labarin na daban Gwamnatin mulkin sojin Myanmar ta yi barazanar dakile huldar diflomasiya da Australia bayan da ta ce ba zata maye gurbin jakadiyarta da ta bar kasar ba .
Gwamnatocin yamma ne suka jagoranci caccakar da ake yi dangane da juyin mulkin da aka yiwa shugaba Aung San Suu Kyi na Myanmar din a shekarar da ta gabata.
A ranar Litinin ne kafafen yada labarai suka ruwaito cewa Australiya tace ba za ta maido da jakadiyarta da ta janye daga Myanmar ba bayan kammala wa’adinta, a maimakon haka, za ta nada wani jami’i da zai yi aiki a madadin jakada.
Mutane sama da dubu daya da dari 7 suka mutu
Kasar da ke kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta fada cikin tashin hankali tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun 2021, inda sama da mutane dubu 1 da dari 7 suka mutu sakamakon amfani da karfi fiye da kima da sojoji masu juyin mulkin suka yi, a cewar wata kungiyar da ke sa ido a kan batun da ya shafi hakkin dan adam a kasar.