Babbar majalisar al’ummar Falasdinawa (PCC) ta sanar cewa, ta yanke shawarar soke dukkan yarjejeniyoyin da kungiyar kwatar ’yancin Palastinawa ta PLO ta kulla da Isra’ila.
Sanarwar na zuwa ne a karshen taron kwanaki uku da majalisar PCC ta gudanar a birnin Ramallah dake yankin yamma da kogin Jordan.
Sanarwar ta ce, sakamakon aniyar Isra’ila na musanta yarjejeniyoyin da aka rattabawa hannu kansu, majalisar PCC ta yanke shawarar soke dukkan wasu hakkoki dake kan kungiyar PLO da hukumomin Falasdinawa suka rattaba hannu a yarjejeniyoyinsu da Isra’ila.
Sanarwar ta kara da cewa, yadda Isra’ila ke ci gaba da mamaya da kuma kwace filaye mallakin Falastinawa na daga cikin dalilan da suka sanya majalisar daukar wannan mataki.
Matakin ya kuma kunshi dakatar da dukkan wasu ayyukan da suke gudanarwa tare da Isra’ila dake shafar harkokin tsaro da soke yarjejeniyoyin ayyukan raya tattalin arziki da duk wasu matakan da Isra’ila ta gabatar dake shafar kwarin gwiwar samar da dawwammamen zaman lafiya.