Majalisar Dokokin Yemen Ta gabatar Bukatar Kafa Doka Ta Haramta Hulda Da Isra’ila.
Majalisar dokokin kasar Yemen ta gabatar da bukatar kafa doka wacce zata haramta hulda da HKI da kuma bayyana hatsarin yin hakan.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan birnin Tehran ta nakalto Murtada Jadban da kuma Dr Ali Alzanam wadanda suka gabatar da bukatar a gaban majalisar a yau, tare da jagorancin mataimakin shugaban majalisar Abdussalam Hashool Zabia.
Labarin ya kara da cewa tuni majalisar ta amince da hakan, ta kuma mika bukatar ga kwamiti kundin tsarin mulkin kasar da kuma sauran wadanda abin ya shafa, don kammala dukkan ayyukan da yakama a yi don tabbatar da shi a matsayin doka cikin kundin tsarin mulkin kasar.
READ MORE : Zaben 2023; Dattawan Arewa Suna Son A Zabi Atiku A Shekara Mai Zuwa.
Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Iraki ce ta fara kafa dokar haramta hulda da HKI a cikin yan kwanakin da suka gabata. Wasu masana suna ganin za’a ci gaba da samun karin kasashen larabawa da musulmi wadanda zasu kafa irin wadannan dokoki a kasashensu.
READ MORE : Iran; Hukumar IAEA Taki Bayyana Hadin Kan Da Iran Ta Bata A Rahotonta Na Baya-Bayan Nan.
READ MORE : Mayakan ADF Sun Kashe Fararen Hula Da Dama A Gabashin Jamhuriyar Congo.