Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar janye dakarun ta na wanzar da zaman lafiya ‘yan kasar Gabon 450 daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayan da aka zarge su da cin zarafi.
Tsawon makonni da suka gabata,an samu wasu daga cikin sojojin kasar ta Gabon dake aikin wanzar da zaman lafiya a Tsakiyar Afrika da aikata laifukan da suka banbanta da ayyukan da aka dora musu a kasar,kazalika ofishin Ministan tsaron kasar ta Gabon a wata sanarwa da ta fitar ta kaddamar da bincike don tattance mutanen dake da hannu a wannan kazamin aiki.
Majalisar Dimkin Duniya da jimawa ta na kokarin wanke ko nisanta kan ta daga duk irin wadanan miyagun dabi’u da suka hada da fyade, azabtarwa, cin zarafi daga duk wani jami’i dake aiki a karkashin ta.
Kasar Gabon na daga cikin kasashe dake da dakarun ta a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika tun bayan barkewar yaki a wannan kasa
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran alfurat News ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Usman alghanimi ya bayyana cewa, a halin yanzu jami’an tsaro sun shirya tsaf domin gudanar da ayyukan tsaro a lokacin tarukan arba’in nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ya ce halin yanzu rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta riga ta gama kammala tsare-tsarenta a bangaren ayyukan tsaro a lokacin wadannan taruka, inda jami’an dubu 20 ne aka ware domin wannan aiki.
Ministan harkokin cikin gidan na Iraki ya ce, ya zama wajibi su dauki irin wadannan kwararan matakan na tsaro, bisa la’akari da matsalolin da aka rika samu a lokutan baya na hare-haren ‘yan ta’adda lokacin tarukan addini a kasar.
Yanzu haka dai jama’a daga sassa daban-daban na kasar Iraki sun fara yin tattaki zuwa birnin Karbala domin halartar tarukan na arba’in da za su gudana a ranar 20 ga wannan wata na Safar da muke ciki.