Majalisar Dinkin Duniya Ta yi Tir Da Harin Da Aka Kai A Masallaci A Kasar Afghanistan.
Babban sakatare Janar din majalisar Dinkin duniya Antonio Guterres yayi tir da harin da aka kai awani masallacin jum’a a birnin Herat dake yammacin kasar Afghanistan inda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 20 tare da jikkata wasu 23,
Kakakin gwamantin Taliban zabuhullah muhajid ya bayyana kashe babban limanin masallacin mawlawi mujib rahman ansari a harin bomb da aka kai a masallacin Guzargha dake birnin heart da misaln karfe 12:40 a jiya juma’a a matsayin harin rashin tausayi da makiya addini suka kai,
Anan sana bangaren babban sakatare janar din majlisar dinkin duniya ya yi tir da mummunan harin kana ya mika ta’aziya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa da fatan zamun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata , kuma nuna cewa ya zama wajibi a kare hakkin gudanar ayyukan Addini a kowanne lokacin a kasar.
READ MORE : Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Ga Duk Wata Barazan A kowanne Mataki.
A gefe guda kuma gwamnatin kasar Iran ta yi tir da harin da aka kai a masallacin juma’art a jiya juma’a abirnin Heart da yayi sanadiyar kashe limanin masallacin da masallata fiye da 20 tare da jikkata wani adadi mai yawa.