Yau ta ke ranar zaman lafiya ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta tsaida domin jaddada manufofin tabbatar da kwanciyar hankali, gami da kawo karshen rikice-rikice, inda ake shafe akalla sa’o’i 24, cikin tsagaita wutar dukkanin tashe-tashen hankulan da ake ciki.
Cikin sanarwar da ta fitar dangane da ranar ta yau, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ya zama dole hukumomi da kungiyoyi suka ci gaba da mutunta dukkanin yarjeniyoyin tsagaita wutar rikice-rikicen da aka kulla a sassan duniya, domin baiwa mutanen da tashe-tashen hankula suka rutsa da su damar samun taimakon da suke bukata, na abinci, da magunguna musamman ma alluran rigakafi cutuka, a daidai lokacin da har yanzu ake fama da annobar Korona.
Majalisar dinkin duniyar ta kuma koka kan cewar, duk da annobar ta Korona ta fi yiwa yankunan marasa karfi illa, fiye da kasashe marasa karfi 100 ne suka rasa samun ko da kaso kalilan daga cikin alluran rigakafin cutar sama da miliyan 687 da kasashe masu arziki suka baiwa al’ummominsu, kamar yadda kididdiga ta nuna a watan Afrilun da ya gabata.
A bangaren muhalli kuwa sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci daukar matakan zaman lafiya tsakanin dan adam da yanayin muhallin sa, domin kuwa matsalar canjin yanayi ba ta dakata ba, duk da takaita walwalar jama’a, da kuma durkusar da tattalin arzikin kasashe da annobar Korona ta janyo.