Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a Libya mai fama da rikici ta yi tayin shiga tsakani don sansanta rikicin siyasar da ya kunno kai tsakanin bangarorin biyu a kasar, bayan da aka samu kafuwar gwamnatoci guda 2 da suka fara gudanar da mulki a baya bayan nan.
Cikin wasu jerin sakwanni da ta wallafa a shafinta na Twitter, Williams wadda take mashawarciya ta musamman ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kan kasar Libya, ta yi gargadin cewa kafa gwamnatoci biyu masu adawa da juna ba shi ne matakin da zai warware matsalar kasar ba.
Jami’ar ta bukaci Majalisar Wakilai da ke gabashin kasar da kuma Majalisar zartaswa mai hedikwata a birnin Tripoli, da su zabi wakilai shida kowannen su, don kafa kwamitin hadin gwiwa domin samar da matsaya kan sansanta rikicin siyasar da ka iya kazancewa.
A wani labarin na daban kuma Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ce yawancin ‘yan siyasar da ke neman kujerar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2023, kamata yayi su kasance garkame a gidan yari.
Tsohon shugaban Najeriyar da ya ki bayyana sunayen ire-iren mutanen da yake nufi, ya ce miyagun ba za su rika yawo cikin walwala ba, idan har hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun yi aikinsu yadda ya kamata, tare da samun goyon bayan bangaren shari’a.
Yanzu haka dai, wadanda ke kan gaba a tsakanin wadanda suka bayyana aniyar neman hawa kujerar Shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa, sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Legas, Ahmed Bola Tinubu, da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki.
Bikin na zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaba Obasanjo ya samu halartar manyan baki cikinsu har da shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma shugaban bankin raya kasashen Afirka AFDB Dakta Akinwumi Adesina.