Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani sojan wanzar da zaman lafiyar ta dan kasar Masar ya mutu sannan abokan aikinsa hudu sun samu munanan raunuka sakamakon hari da bama-bamai da aka kai kan jerin gwanon motocinsu a arewacin kasar Mali mai fama da tashin hankali ranar Asabar.
Guterres ya ce hare -haren na iya zama laifukan yaki, don haka ya yi kira ga hukumomin Mali da su “ba da himma” wajen gano wadanda ke da alhakin hakan.
Kasar Mali dake fama da hare-hare daka masu ikirarin jihadi, ta fada cikin rudanin siyasa tun bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a watan Agustan shekarar 2020, inda aka kafa gwamnatin farar hula ta wucin gadi, wanda itama aka sake hambarar da ita a karo na biyu kasa da shekara guda.
A wani labarin na daban rundunar sojin Faransa, ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka mayakan ‘yan ta’adda 30 a Mali, yayin farmaki kashi 2 da suka kaddamar kansu a ranakun Alhamis zuwa Juma’ar da suka gabata.
A watan Disambar da ya gabata ma, sojojin na Faransa sun halaka mayakan ‘yan ta’adda akalla 33 a kasar ta Mali, yayin farmakin da ta kaddamar kansu akan iyakar kasar da Mauritania.
Yanzu haka dai Faransa na da dakaru dubu 4 da 500 karkashin rundunar Barkhane a Mali, wadanda ke taimakawa dakarun majalisar dinkin duniya akalla dubu 13 dake kasar.
A baya bayan nan ne dai Ministar tsaron Faransa Florence Parley ta sanar da shirin tura karin sojin kasar 600 zuwa Mali domin murkushe hare-haren ta’addancin dake karuwa a yankin Sahel.