Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kulla yarjejeniya da jami’an Rasha da na Ukraine don gudanar da aikin kwashe fararen hular da suka makale a masana’antar sarrafa karafa ta Azovstal da ke birnin Mariupol, sakamakon yakin da ake cigaba da gwabzawa.
Kakakin ofishin ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya Saviano Abreu, ya ce tun a ranar Juma’a aka cimma yarjejeniyar tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross.
Abreu ya kara da cewar tun da safiyar ranar Asabar tawagar jami’an ceto suka isa masana’antar sarrafa karafan da ke birnin na Mariupol, ba tare da yayi karin bayani kan aikin ba, saboda kare lafiyar wadanda aka kwashe da ayarin motocin.
A wani labari na daban karshen watan Afrilu, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bukatar tsagaita wuta a yankin Ukraine domin rage radadin illar yakin ga jama’ar kasar da kuma na duniya baki daya.
Guterres ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Sakataren Harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a birnin Moscow.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bukatar tsagaita wuta a yankin Ukraine domin rage radadin illar yakin ga jama’ar kasar da kuma na duniya baki daya. Guterres ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Sakataren Harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a birnin Moscow.
Yace, “Na san cewa ayau muna fuskantar matsaloli masu sarkakiya a Ukraine, da kuma fassara abinda ke faruwa ta fuskoki daban daban, akan assalin abinda ke faruwa a Ukraine”.
Guterres ya kara da cewa, Matakin bai kai ga dakile fatar samun tattaunawa ta hakika akan hanyar da tafi dacewa a bi domin takaita radadin da jama’a ke fuskanta ba.
A daya bangaren, Sakatare Janar din ya nuna matukar bukatar neman hanyoyin da zasu samar da shirin tatatunawa, da samar da yanayin shirin tsagaita wuta a cikin gaggawa da kuma samar da hanyar kawo zaman lafiya mai dorewa.
Yace, “Kuma akan wannan hanyar muna son yin duk abinda ya dace domin takaita illar yakin a kowane sashe na duniya”.