Akwai yiwuwar mai tsaron ragar Arsenal Bernd Leno ya shirya barin kungiyar, a yayin da Aaron Ramsdale ya shirya tsaf don karbe matsayinsa a lamba daya.
Yanzu dai Leno ya fara gamuwa da kalubale kenan, saboda akwai alamar zai fara dumama benchi, don haka zai fara neman canza sheka zuwa inda zai rika buga wasa a kai a kai.
Arteta ya yi ta yaba wa Ramsdale, mai tsaron ragar da aka saya a farkon wannan kaka a kan fam miliyan 30 bayan nasarar Arsenal ta farko a wannan kaka, kuma ana sa ran dan wasan na kasar Ingila ya ci gaba da kasancewa a ragar Arsenal.
To tun bayan wasannin karshen makon da suka gudana a gasar Firimiyar Ingila Arsenal ke shan caccaka daga magoya bayanta, masu sharhi, da kuma tsaffin ‘yan wasa ciki har da nata, sakamakon rashin nasarar da tayi da kwallaye 2-0 a hannun Chelsea.
Yayin da yake tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki, tsohon dan wasan Arsenal Bacary Sagnia da ya buga mata wasanni 284, ya caccaki dukkanin masu ruwa da tsaki a shugabancin kungiyar inda yace muddin suka ci gaba da son rai da kuma nuna halin ko in kula dangane da sayen ‘yan awsan da suka dace, to fa ba s hakkah za su ci gaba shan kaye a wassanin da ke tafe.
A cewar Sagnia abin bakin ciki ne ganin yadda kimar tsohuwar kungiyarsa tasa ya zube duk da irin ficen da tayi a zamaninsu da kuma na wadanda suka gabace su.
Sai dai kocin Arsenal Mikel Arteta ko a jikinshi wai a tsikari kakkausa, domin kuwa yayin martini kan caccakar da ake musu cewa yayi, ko da wasa bai damu da bacin rai ko sukar kowa ba kan rashin nasarar da suka yi a wasansu da Chelsea.
A cewar mai horaswar abinda yake bukata shi ne ‘yan wasan da za su fuaknci kalubalen da ke gabansu tare da kawo karshensa.
A ranar 28 ga wannan watan Arsenal za ta kara da Manchester City.