Yoon Suk-yeol mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ya lashe zaben shugabancin kasar Korea ta Kudu, wanda ya gudana a ranar Alhamis.Jim kadan bayan samun nasarar ce, sabon shugaban ya sha alwashin daukar matakan da suka dace wajen tunkarar matsalar shirin nukiliyar Korea ta Arewa.
Tuni dai Lee Jae-myung na jam’iyyar Democrat mai mulki ya amince da shan kaye.
Alkaluman hukumar zaben sun kuma nuna cewar, kashi 77.1 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri’a ne suka fito zaben shugabancin kasar ta Korea ta Kudu mai yawan mutane kimanin miliyan 52.
Kafin nasarar da ya samu, sabon shugaba Yoon Suk-yeol, wanda bai taba rike mukamin siyasa ba, ya kasance tsohon babban mai gabatar da kara na Korea ta Kudu.
Yoon wanda ya sha alwashin “murkushe” barazanar gwamnatin Korea ta Arewa da ke karkashin Kim Jong Un y ace kofar tattaunawa a bude take,” tsakanin kasashen makwaftan juna, dangane da sabanin da ke tsakaninsu, musamman kan shirin nukiliyar da ke tayar da hankulan kasashen duniya.
A bangaren nabaran wasanni kuma An dakatar da cinikin kungiyar Chelsea kamar dai yada mammalakin wannan kungiya dan kasar Rasha Abramovich ya bukaci a yi a baya.Daukar wannan mataki daga gwamnatin Birtaniya na zuwa ne bayan da hukumomin suka dau wasu sabin takunkumai sanadiyyar yaki da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine.
Tun bayan da Rasha ta kaddamar da wannan mamaya zuwa Ukraine, mammalakin wannan kungiya ta Chelsea duk da nuna damuwar sa a kai, Abramovich dan shekaru 55 babu sunan sa daga cikin mutanen da suka fuskanci wata barrazana daga kasashen Duniya.
Soke batun cinikin wannan kungiya ta Chelsea da gwamnatin Birtaniya ta yi na zuwa a wani lokaci da Rasha duk da zaman tattaunawa da aka soma,na saka attajirin Abramovich cikin wani yanayi marar kyau,duk da cewa gwamnatin Birtaniya ta sanar da daukar wasu jerryn matakai na yin sassauci ga kungiyar ta Chelsea tare da bata damar ci gaba da taka tamola a fagen gasar ta Frimiya ta Ingial.
A karshe yanzu kam kungiyar ta Chelsea na fatan shiga tattaunawa da hukumomin Birtaniya don ganin an cimma mafita a kan wannan matsalla.