Alawah Baitam mai fasahar rubutun larabcin ya shara a kasar Morocco da salon rubutun larabci iri-iri mai kayatarwa, wanda yake yi a kan abubuwa daban.
An haife shi a garin Ainul Tutah a shekara ta 1958, sannan kuma ya fara hardar kur’ani mai tsarki tun yana da shekaru 6a duniya, ya kammala hardar kur’ani baki daya yana da shekaru 12 a duniya.
Mai fasahar rubutun larabcin a halarci makarantun kur’ani daban-daban, akasarinsu makarantu ne na zawiyya, ko kuma makarantun allo kamar yadda aka fi saninsu a kasar Hausa, wanda irin wadanna makarantu sun samo asali ne dama daga kasashen larabawa na arewacin Afirka.
baya ga rubutun kur’ani, Alawah Baitam ya kasance mai matukar shawa’ar ilimin adabin larabci da kuma abubuwa da suka shafi tarihin larabawa, musamman wakoki da ake tsara su a cikin baituka na hikima.
A kan haka ya yi rubu kan adabin larabawa da tarihinsu da kuma tarihin muslunci a wakoki da yawansu ya kai baitoci 2894, wadanda suke a cikin littafan da ya rubuta a wannan fage.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Alahad cewa, a yau an gudanar da janazar babban malamin addini Allamah Abdulamir Qabalan a birnin Beirut na kasar Lebanon.
Taron janazar dai ya samu halartar jama’a da dama, da suka hada jami’an gwamnati, malamai na addinin muslucni da kuma kiristoci gami da kabilu daban-daban na kasar Lebanon da suka hada da ‘yan Duruz da Arman.
A ranar Litinin da ta gabata ce Allah ya yi wa Allamah Qabalan rasuwa bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Tun bayan bacewar shugaban majalisar mabiya mazhabar ahlul bait a kasar Lebanon Imam Musa Sadr, a kasar Libya, bayan da tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi ya gayyace shi, mataimakinsa Allamah Qabalan ya ci gaba da jagorantar lamurran majalisar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron janazar a yau Talata akwai wakilan shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon, baya ga haka kuma wasu daga cikin ministoci gami da malaman addini na shi’a da sunnah sun halarci wurin.
Allamah Abdulamir Qabalan dai ya kasance mai goyon bayan hadin kan al’ummar kasar Lebanon, wanda hakan ne ya bashi matsayi na musamman da girmamawa daga dukkanin al’ummar kasar.
baya ga haka kuma ya kasancea sahun gaba wajen mara baya ga gwagwarmayar al’ummar kasar wajen yaki da mamayar da Isra’ila ta yiwa kasar har zuwa lokacin da kungiyar Hizbullah ta fattaki Isra’ila daga Lebanon.