Gwamnatin Burkina Faso, ta ce tawagar jami’an agajin da suke aikin zuke ruwan da ya mamye wani ramin hakar ma’adinin Zinc, suna dab da kaiwa ga ceton mahakan ma’aikata takwas suka makale kusan wata guda a cikin ramin, domin dauko su daga wani sako da suka shige domin samun mafaka.
Mahakan ma’adanan da ambaliyar ruwan ta rutsa da su dai sun hada da ‘yan Burkina Faso 6, dan Tanzania daya da kuma dan Zambia daya, wadanda suka bace tun bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye filin hakar ma’adanin Zinc na wani kamfanin kasar Canada da ke garin Perkoa tun a ranar 16 ga Afrilu.
Kamfanin ya ce yayin da akasarin ma’aikatan da ke karkashin kasa suka samu nasarar tsira daga ambaliyar, sauran guda takwas sun gaza fita ne kasancewar suna da nisan mita 520, kwatankwacin kafa dubu 1 da 706 daga doron kasa.
Tun a ranar larabar da ta gabata, kakakin gwamnatin Burkina Faso, Lionel Bilgo ya ce an cire ruwan da yawansa ya zarce lita miliyan 38, a kokarin da ake yi na ceto ma’aikatan da ambaliya ta rufe a ramin hakar ma’adanan da suke tsaka da aiki a cikin sa.
A wani labarin na daban Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci taimakon gaggawa daga masu bada agaji domin taimakawa ‘yan Nijar sama da miliyan biyu dake fama da matsalar karancin abinci da ambaliyar ruwa da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
David Carden, jami’in kungiyar agaji ta Majalisar da ya ziyarci Nijar, yace suna bukatar akalla Dala miliyan 523 domin taimakawa mutane miliyan 2 da dubu 100.
Jami’in yace Nijar na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da na jinkai da matsalar tsaro da kuma tashe tashen hankulan da Yan bindigar ke haifarwa wajen kai hari kan fararen hula abinda ya haifar da talauci a cikin jama’a.
Carden yace annobar korona ta dada jefa al’ummar kasar cikin mummunan yanayi inda suke bukatar taimako sosai, yayin da yaran dake tsakanin watanni 6 zuwa shekaru 5 a duniya da yawan su ya kai 457,200 ke fama da tamowa.
Jami’in yace ziyarar da ya kai kasar ta bashi damar ganewa idan sa halin da irin wadannan mutane ke ciki, yayin da kuma ya ziyarci Ouallam dake arewacin birnin Yammai inda Yan bindiga suka kasha fararen hula 100a kauyuka guda 2 ranar 2 ga watan Janairun da ta gabata.